Home / Labarai / AN Rufe Masallacin Kasa Na Abuja

AN Rufe Masallacin Kasa Na Abuja

Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Sakamakon irin matsalar da ake kauce ma faruwarta ta fuskar yada cutar da ke toshe numfashi ta (Covid 19) Korona birus yasa hukumar gudanarwar babban masallacin kasa da ke Abuja suka bayyana rufe masallacin da a yanzu ba za a gudanar da salloli biyar da ake yi a masallacin ba.
Hukumar gudanarwar ta bayar da sanarwar ne a yau Litinin 23 ha watan Maris, 2020. Inda suka bayyana a cikin wata sanarwar da hukumar gudanarwar ta masallacin suka sanyawa hannu sun bayyana cewa hatta da budaddiyar kasuwar da ke masallacin da wurin cin abinci duk an rufe su baki daya har sai abin da hali ya yi domin ba a bayyana ranar bude masallacin ba.

About andiya

Check Also

Trafficking: NAPTIP seeks more collaboration, advise potential victims

  By Suleiman Adamu, Sokoto The National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person(NAPTIP) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.