Home / Labarai / An Sa Gasar Kudi A Kan Cin Bashin Gwamnati A Arewa Maso Yamma

An Sa Gasar Kudi A Kan Cin Bashin Gwamnati A Arewa Maso Yamma

Daga Imrana Abdullahi

An yi kira ga daukacin al’ummar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya da su himmatu wajen bayyana ra’ayoyinsu a rubuce ko ta hanyar fadin magana da muryarsu a game da batutuwan tsananin cin bashin da Gwannatocin Jihohin arewacin Najeriya kan yi musamman ma a yankin Arewa maso Yamma.

Babban Daraktan AID Foundation Emmanuel Bonet ne ya fayyace hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a dakin taron na cibiyar yan jaridu ta kasa reshen Jihar Kaduna a ranar 29 ga watan Janairu, 2024 da nufin fadakarwa ga jama’ar yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Kungiyar ” Aid foundation”, ce ta Sanya wannan gasar da al’ummar arewacin Najeriya za su yi a kan ko mutum na ganin ya dace Gwannati ta ci bashi ko a’a.

Ana bukatar dun wanda ke bukatar shiga wannan gasar da aka Sanya makudan kudi naira dubu dari Bakwai, da ake saran kowace Jihar a yankin Arewa maso Yamma duk wanda ya samu nasara za a  bashi kudi naira dubu dari daya idan ya lashe gasar.

“Ba sai lallai an ci bashi ba kuma ba sai lallai an musgunawa al’umma ba wajen karbar haraji”,

Sai mutum ya rubuta ga hanyoyin da ya dace abi wajen samun kudin da Gwamnati za ta yi amfani da shi.

” Kuma wannan gasar za ta fara ne daga yau Litinin 29 ga watan Janairu, 2024 ta kuma kare a ranar 15 ga watan Mai zuwa na Fabrairu 2024, kuma masu bukatar yin gasar za su shiga shafin yanar Gizo na Aid Foundation, wato @aidfoundation an kuma raba abin kashi biyu ga duk maganar da mutum ke son yi kada ya wuce minti biyu, haka kuma idan kana son rubutawa kada ya wuce kalamomi dari biyu.

Saboda haka ya duk mai son shiga gasar idan ya shiga yanar Gizo na Aidfoudation zai ga abin da aka rubuta an yi da harshen Turanci an kuma yi da harshen Hausa, don haka ba lallai bane sai a harshen Turanci mutum zai iya rubutawa idan mutum na so ko a harshen Turanci ma za a iya rubutawa ka kuma samu nasarar lashe gasar.

Muna kokarin yin fadakarwa ne game da abin da Jihohinmu suke karba na cin bashi, saboda haka a ranar Goma sha daya na watan da ya gabata ne aka fara yin fadakarwa ga jama’a game da bashin da Jihohi ke karba a madadin mu.

“Aid Foundation ta fara fadakar da jama’a a kan irin yadda jama’a za su gane  bashin da kowace Jiha ke ci da kuma nawa ne kuma yaya za su biya bashin kuma yaya bashin ya kasance, sannan kuma yau.

“A yau mun zo ne domin karawa jama’a karfin Gwiwa Kan cewa akwai wani kudi kalilan da aka Sanya ake son ayi gasa a kai, ga duk wanda ke da tunanin cewa bai dace ba Gwannati ta ci bashi ba domin za ta rika samun kudin dabza a rika yin ayyuka da shi, saboda an gano cewa mutane da yawa na da wannan tunanin amma ba su da hanyoyin da za su iya gayawa Gwannati shi yasa muka ce bari mu yi wannan gasar domin ba mu son muyi gasar haka kawai sai muka ce bari mu kawo karamin kudin da muke da shi ga wanda ya samu nasarar zama na daya, biyu da na uku za a iya ba su wani abu. Sai aka Sanya kudi dubu dari Bakwai kowace Jiha za ta ci dubu dari don haka muna neman ne al’umma su zauna su kuma yi nazari me za su iya yi wace gudinmawa za su iya kawo wa su ba Gwamnati cewa mai Makon cin bashi za a iya yin kaza da kaza a samo kudi ba lallai sai an ci bashi ba kuma ba sai lallai an musgunawa al’umma wajen haraji ba, ha hanyoyin da za a iya samun kudi kuma ga ayyukan da za a iya yi da kudin.

Kuma za a yi rubutun bayanin ne a cikin yawan kalmomin da ba su wuce dari biyu ba, 200 idan kuma yin magana ne mutum zai yi kada maganar ta wuce mintuna biyu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.