Home / Labarai / An Samu Yan Takara Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano  

An Samu Yan Takara Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano  

An Samu Yan Takara Masu Ta’ammali Da Miyagun Kwayoyi A Kano
Mustapha Imrana Abdullahi

A kokarin ganin an tace harkokin siyasa daga masu shan kwayoyi a zaben da za a yi na kananan hukumomi a Jihar Kano yasa Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta yi gwajin tu’ammali da kwayoyi ga ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi na jam’iyyu daban-daban a Kano.

Jami’in da ke kula da hukumar a Kano Ibrahim Abdul ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Kano cewa ‘yan takara 250 ne aka yi wa gwajin, inda aka gano wasu daga ciki nada alamun tu’ammali da kwayoyi.

Ibrahim Abdul yace tantance ‘yan takarar shugabancin kananan hukumomi, mataimakansu da kansiloli, nada nufin kakkabe ‘yan kwaya a cikin zababbun shugabanni a jihar.

A ranar 16 ga watan Janairun badi, 2021 ne za a gudanar da zaben kananan hukumomi a Kano.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.