Home / Labarai / An Shirya Taron Fadakar Da Matasa Illar Shaye Shaye A Rayuwarsu

An Shirya Taron Fadakar Da Matasa Illar Shaye Shaye A Rayuwarsu

 

Daga Imrana Abdullahi
Kungiyar Tabbatar da Zaman Lafiya da inganta harkokin rayuwa mai suna  (Global Peace and Life Rescue Initiative) sun shiryawa matasa masu ta’ammali da miyagun kwayoyi taron fadakarwa da kuma tattaunawa na kwanaki biyu a karamar hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar kaduna.
Kungiyar tare da hadin Gwiwar ma’aikatar tsaro ta kasa da ke Abuja ne suka shirya wannan babban taron fadakarwa da ilmantar da dimbin matasan da aka halarta kuma suka halarci taron da aka yi a babban dakin taro na gidan tunawa da marigayi Sardauna da ke Kaduna.
Da yake tattaunawa da manema labarai a wajen taron shugaban kungiyar Ambasada Dokta Melvin Ejeh ya shaidawa manema labarai irin farin ciki da dimbin godiyar da suke yi wa shugaban rundunar Sojan Najeriya Janar CG Musa bisa irin gagarumin taimakon da yake ba su wajen tafiyar da wannan aikin da za su yi a duk fadin kasa baki daya amma a yanzu sun fara ne da Jihar Kaduna.
” Muna kokarin ceton lafiya da rayuwar wadannan matasan ne da suke rayuwa cikin al’umma muna nuna masu cewa suma suna da muhimmanci kwarai don haka muke kokarin raba su da wannan shaye shayen”.
Dokta Melvin Ejeh ya kuma ci gaba da bayanin cewa a gobe idan Allah ya kai mi za su yi wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki tare da wadannan bayin Allah su gaya masu har yadda suke samun wannan kayan shaye shayen da suke yin ta’ammali da su.
” Mun samu nasarar samun a kalla matasa guda Hamsin da a halin yanzu suke karbar horo a kan al’amuran rayuwa da sana’a daban daban tare da barin hanyar shaye shaye domin mun ga ne cewa kame kamen masu shaye shayen nan ba shi ne mafita ba saboda haka ne muka bullo da wannan tsari kuma muna da wurin gyaran halin duk wani mai yin shaye shaye a Jihar Filato inda za mu ajiye su a wurin kwanansu mai kyau ana kula wa da su da niyyar raba su da shaye shayen baki daya ta yadda za su koma cikin al’umma a matsayin ingantattun sahihin mutane da kasa za ta yi alfahari da su kuma su zama manyan gobe da za su bayar da gudunmawarsu wajen ciyar da kasa da nahiyar Afirka gaba baki daya”.
Wannan kungiya tare da hadin Gwiwar wadansu kungiyoyin duniya ne ke bayar da gudunmawa ana aiwatar da irin wadannan shirye shiryen da ake yi a halin yanzu
Wanda is zuwa yanzu har muna da matasa a kalla guda Hamsin (50) da ake ba su horo a yankin Kudancin Kaduna duk bisa kokarin babban Hafsan hafsoshin sojan Najeriya kuma muna godiya gare shi kwarai.
Muna son fadakar da matasa masu shan kwayoyi ne game da batun illar shaye shayen da suke yi.
“Muna kiran ainihinasu shan kwaya da za su tattauna da su mu kuma bayar da lambobin waya ga duk mai shan kwaya ya kira ya gaya mana”.
Za mu kira ainihin masu ruwa da tsaki da shugabannin jama’a domin a tattaunawa da su ainihin yin magana a cikin batun shaye shaye kuma za a yi hakan ne ba a bayyane ba a cikin sirri za a yi.
Kuma za mu kai su wurin da za a ajiye su a wurin ajiyar masu irin wannan batun
” A halin yanzu mun samu mutane 50 da muke ba su horo na musamman domin samun gyaran su baki daya
Abubakar Alhaji Garba daga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wanda ya wakilci shugaban hukumar na kasa Birgediya Janar Muhammadu Buba Marwa, lacca ya bayar lokaci mai tsawo a wurin taron a kan yadda kwayoyi da sauran kayan maye suke da kuma illolinsu da kuma irin yadda ta’ammali da miyagun kwayoyi ke yi wa iyaye da sauran jama’a illar lalacewar dukiya, lafiya da kuma samun matsalar tattalin arzikin masu shaye shaye inda ya tabbatarwa da taron cewa a halin yanzu akwai wadanda ke hannunsu ana duba su tare da yi masu magani
Batun shaye shaye na kawo matsalolin rayuwa da lalacewar tattalin arzikin kasa da tabarbarewar jama’a da yawa
Shi yasa muka yi wa wadannan matasa cikakkiyar fadakarwa da nufin samun gyara
Muna yin aiki a kan iyakokin Najeriya duk inda kaje zaka ga mutanen NDLEA suna gudanar da aiki
Iyaye su rika bayar da cikakkiyar kulawa ga yayansu domin kada su kasance a cikin wannan yanayi na shaye shaye a cikin al’umma musamman ma a tsakanin matasan da ake da su
Shaye shaye illace da ta shafi gwamnati, iyaye da sauran al’umma kuma da wahala Gwambati ta iya aiwatar da wannan aiki, masu shaye shaye da suke yi suna yin asarar dukiya da dama ta iyaye da sauransu
Duk hanyoyin da ke cikin iyakokin Najeriya muna nan muna aiki kuma muna gano su ta hanyoyin aiki da dama da muke da su, muna kama masu safarar kwayoyi daga wata Jiha zuwa wata Jiha kuma muna yin wa’azin musulunci da na Kirista domin a fadakar ta hanyar addini ta yadda za a Ceci rayuwar jama’a

Da yake ganawa da manema labarai a wurin taron shugaban hukumar wanzar da zaman lafiya ta Jihar Kaduna Dokta Sale Momale, cewa ya yi hakika wannan taron da aka shirya wa matasa abin farin ciki ne da ya dace kowa ya yi farin ciki da shi saboda irin matsalar da shaye shaye ke yi wa matasa na haifar da illoli daban daban wanda hakan ma na ba su damar aikata miyagun laifuffuka a Jihar Kaduna.

Abin da ke haifar da aikata laifuka a Jihar Kaduna da ma sauran wadansu bangarorin Najeriya shi ne amfani da miyagun kwayoyi.

” Alhamdulillah irin wannan tara matasan a wuri guda da suka fito daga lungu da sako na jiha a kawo hankalin su abu ne mai muhimmanci wanda muke bayar da goyon baya da cikakken hadin kai da hakan.Muna yin kira ga kungiyoyi da hukumomin Gwamnati da su hada kai da wannan tsarin da babban Hafsan hafsoshin Najeriya ke bayar da gagarumar gudunmawa domin samun nasarar da ake bukata”.

Ta suke tofa albarkacin bakinsu matasan da aka shiryawa taron da suke cikin matsalar shaye shaye sun bayyana Gamsu da kuma bayanin cewa an dai tara su ne a yi masu wa’azi da fadakarwa a kan illar abin da suke yi, wasu sun yi magana da manema labarai a cikin harshen Turanci da hausa.

Taron dai ya samu mahalarta daga hukumomin tsaro na Gwannatin tarayya da na masu zaman kansu da suke yin aiki a cikin al’umma da suka hada da Yan Sandan farin kaya DSS, Jami’an Yan Sanda masu sanye da Yunifom, Rundunar sojoji, da kuma jami’an Peace Corp da dai sauransu da suka hada da kungiyoyin da ke aiki a cikin al’umma daban daban.

Sauran mahalarta taron sun hada da Sarakuna da Limamai da Malaman addinin Kirista da na musulunci duk baki daya inda suka zauna tare cikin dakin taro daya da wadannan matasan da ake yin abin domin su da su canza su zama mutanenkirki da za a iya yin alfahari da su a cikin al’umma.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.