Home / Labarai / An Soke Shagulgula, Hawan Sallah A Katsina

An Soke Shagulgula, Hawan Sallah A Katsina

An Soke Shagulgula, Hawan Sallah A Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi
Mai martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya tabbatar da soke yin shagulgula da kuma hawan Sallar da aka saba yi a lokacin karamar Sallah.
Sarkin Katsina ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Sakataren masarautar Alhaji Bello M Ifo, Sarkin yakin Katsina da aka rabawa manema labarai.
Ssrkin Katsina ya ce saboda irin iftila’in da ake fama da shi na kashe kashe da Sace sacen jama’a ya zama dole a soke wannan hawan Sallah a halin yanzu a maye gurbinsa da gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah game da wannan matsalar.
“Bisa shawarwarin da muka samu daga Gwamnati,jami’an tsaro da kuma ma’aikatar lafiya ta Jiha ya Sanya a halin yanzu qn Soke yin hawan Sallah da shagulgulan da aka saba yi a duk lokacin karamar Sallah”, in ji takardar.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.