Kokarin da ake yi a Jihar Kaduna bayan tattaunawa da dukkan bangarori da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi karkashin Gwamna Uba Sani wanda aka samu ingantar al’amuran tsaro ya sa aka yi kira ga sauran Jihohi da su yi ko yi da Jihar Kaduna, saboda suma suna fuskantar irin wannan matsalar.
Mai bayar da shawara na musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani a kan bunkasa karkara Alhaki Shehu Aminu Abdullahi ya ce irin yadda Jihar Kaduna ta dauki matakin da ya dace a game da harkokin tsaro idan Jihohi suka dauki wannan mataki na Jihar Kaduna hakika za a samu gagarumin ci gaban da kowa yake bukatar samu.
Ya ce aikin wanda ya hada dukkan sauran jama’a musamman masu ruwa da tsaki a Jihar da wadanda ake zargi da laifin ta’addanci na satar jama’a, aka tattauna wannan tsarin zai taimakawa Jihar Kaduna da al’ummarta da zai taimakawa ci gaban Dimokuradiyya.
Da yake yin jawabi ga manema labarai a ranar Litinin a Kaduna, bayan ya dawo wajen zagaye a karamar hukumar Giwa, Alhaji Abdullahi ya bayyana wannan kokari na Gwanna da cewa abin a yaba ne saboda an bayar da muhimmanci ga yin aiki tare da jama’a an kuma yi kokarin inganta tattalin arzikin jama’ar Jihar.
Mai bayar da shawarar a kan yadda za a bunkasa harkokin yankunan karkara ziyarar da ya kai ya yi ya bashi damar sanin irin yadda al’amura suke ciki a karkara musamman ma a wuraren da ya ziyarta, da suka hada da batun samar da Tituna da Gadoji da dai sauran abubuwan more rayuwa wadanda ya gani kuma yake shaidawa Gwamnati domin daukar matakan gaggawa ta hanyar kawo dauki.
Kamar yadda ya ce, kokarin Gwamnatin na samar da ababen more rayuwa, musamman ma a fannonin da a can baya suka kasance suna fama da matsalar yan bindiga da satar mutane wanda a halin yanzu suke ganin ci gaban harkokin rayuwa baki daya, da yawa daga cikin al’ummar wadannan wuraren sun dawo yankunan su da a can baya suka tsere suna yin Gudunhijira a wadansu wurare sakamakon matsalar tsaron da ta faru a can baya, wadansu abubuwan da a can baya aka yi watsi da su a halin yanzu suna dawowa a hankali duk a karkashin Gwamnatin jihar Kaduna karkashin Sanata Iba sani.
Wanda ya kasance ya na da rajistar hukumar kula da harkokin Kwantiti Sabe na Filaye ta (FNIQS), Alhaji Abdullahi ya bayar da shawara ga wadanda suka kasance sun yin kalubale ga wannanbtsarin tattaunawa ta harkar tsaro da babu daukar makami sai tattaunawa da nufin samar da zaman lafiya na din- din- din ya dace su Sani cewa idan ba zaman lafiya babu wata al’ummar da za ta samu ci gaba, sai ya kara da cewa ko a zamanin yaki, batu zaman lafiya dole shi ne a Gaba, kamar yadda ya bayyana filla filla.
Saboda haka sai ya yi kira ga sauran daukacin Jihohi da Gwamnatin tarayya da su yi ko yi da wannan tsarin na Gwamnan Jihar Kaduna ta yadda za a samu zaman lafiya a kasa baki daya.
Alhaji Aminu ya ce a koda yaushe Gwamna Sanata Uba Sani na kokarin samar da hanyoyin samun sauki da daukacin al’umma, misamman ta hanyar gyaran abubuwan amfani na cikin gida domin inganta rayuwa da kuma kara habbaka tattalin arzikin kasa da ke ba jama’a dama mara iyaka, saboda idan da akwai zaman lafiya za a iya taimakawa kowa, Lamar yadda ya tabbatar.
Sai ya yabawa Gwamna Uba Sani bisa irin yadda yake tunkarar al’amura wanda sakamakon hakan ake samun zaman lafiya a daukacin Jiha baki daya, ya kara da cewa ko ziyarar sa a matsayin mai bayar da shawara ta musamman a kan bunkasa karkara, Honda ya halarci Giwa, Yakawada, Gadagau, Oatika, Bataro da dai sauransu duk a karamar hukumar Giwa, hakika wannan sakamako ne na aiki tukuru na Gwamna Sanata Uba Sani da Gwamnatinsa a Jihar Kaduna baki daya.