Home / Labarai / An Yi Kira Ga Daukacin Yan Nijeriya Su Zabi Masu Mutunci

An Yi Kira Ga Daukacin Yan Nijeriya Su Zabi Masu Mutunci

Mustapha Imrana Abdullahi
Alhaji Shehu Dalhatu ya yi kira ga daukacin al’ummar Nijeriya da su tabbatar sun zabi wadanda suke yayan mutane wato wanda yake dan mutane da ke da mafadi ba masu kunnen kashi ba.
Shehu Dalhatu ya yi wannan kiran ne lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a wajen babban taron tunawa da marigayi Dokta Yusuf Mai tama Sule da aka yi a garin Gumel domin fadakar da matasa muhimmancin sanin wanda ya dace su ba hadin kai da goyon baya a lokacin kowane zabe.
Dalhatu ya ci gaba da cewa ya zama wajibi ga dukkan al’umma da su himmatu wajen zaben mutumin kwarai da zai shugabanci su a kowane irin mataki.
” Kada a rika zaben mutane masu kunnen kashi da ba su da mafadin da zai yi magana idan sun dare madafun iko”, inji shi.
Ya kara da cewa sai kaga mutane na tafiya su na magana su kadai sakamakon halin matsin da suke ciki, kuma ba a da niyyar samawa jama’a hanyar samun sauki don haka kowa ya tabbatar da zaben mutanen kirki.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.