Home / News / Ba Zan Tsaya Takara Ba – Muntari Lawal

Ba Zan Tsaya Takara Ba – Muntari Lawal

 

Mustapha Imrana Abdullahi
Alhaji Muntari Lawal ya fito fili ya bayyana cewa babu inda ya ta ba cewa ya na son tsayawa takarar neman wata kujera.
Alhaji Muntari Lawal ya Karyata batun zai tsaya takara ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Katsina.
Muntari Lawal ya ce kamar yadda ya Sani shima wasu mutane ne suka aiko masa tun da farko ta hanyar dandalin Sada zumunta cewa ga fastocinsa ko’ina a cikin garin Katsina ana cewa ya tsaya takara ba wai zai tsaya ba har masu wannan niyya sun yanke hukunci kawai.
“Ni ba ni da wata niyyar yin takara kuma ban cewa kowa zan tsaya takara ba don haka masu yin wannan yunkuri su na son hada ni fada da mutane ne kawai don ban ce zan tsaya takara ba, kuma ai akwai shugaba na shi ne Gwamnan Jihar Katsina kuma duk abin da ya yanke hukunci shi za a yi daman can tare aka gan mu, kuma ni na amince da shugabancinsa don haka ban ce zan tsaya takara ba sam”, inji Muntari Lawal.
Muntari Lawal ya ci gaba da cewa masu yada wannan fastoci cewa zan yi takara duk ba wanda ya shawarce ni kuma ni ban san da wannan magana ba don haka tuni na Sanya ayi Mani bincike a gano masu yin wannan aiki da ke kokarin hada ni da wasu mutane.
“An ga irin yadda muka gudanar da zaben shugabannin jam’iyya a Jihar Katsina kuma kowa ya yaba aikin da muka har Abuja duk sun ya ba mana shi ne wasu ke son kawo wata hanyar hadin fada yin da an ga waccan da duk wani tarkon da aka Dana bai kama ba, sai ake kokarin bullowa da hanyar zan yi takarar Sanatan Katsina ta tsakiya, ni ban taba yin takara ba kuma tun shekarar 1979 nake cikin harkar siyasa sau daya kawai na tsaya takarar kai da halinka ban ji dadi ba domin abin bai yi Mani dadi ba na kuma ce ba zan kara yin takara ba”.
” zan kuma duba sosai idan na gano masu yin wannan to, idan wadanda zan yi wa magana ne ko ma in je har gida kuryar daki in gaya masu magana zan yi domin ba ni na Sanya su ba”.
Muntari Lawal ya kara da bayanin cewa ya na son tabbatarwa jama’a cewa jam’iyyar APC ta yi masa komai ta yi masa Riga da Wando da komai kuma mafi yawan wasu mutanen ma dalilin mulkin APC ne suka sanshi don haka sai ya kara  yi wa Allah godiya bisa taimakon da yake yi masa.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.