Home / News / An Yi Taron Lallashi Da Ban Hakuri A Mazabar Kujama

An Yi Taron Lallashi Da Ban Hakuri A Mazabar Kujama

An Yi Taron Lallashi Da Ban Hakuri A Mazabar Kujama

Mustapha Imrana Abdullahi
Yayan jam’iyyar APC na mazabar Kujama da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna sun yi taron lallashin yayan jam’iyyar domin kowa ya taho a hada kai ta yadda za a samu nasarar lashe zaben shugaban karamar hukumar Chikun a zaben kananan hukumomin da za a yi a Jihar kaduna.
Taron da aka yi karkashin Muhammad Rabi’u Musa, jigo a jam’iyyar APC ya samu halartar dimbin magoya baya inda aka yi kira ga kowa da ya amayar da korafin da ke cikinsa domin a samo hanyoyin gyara ta yadda za a ta fi tare a cimma nasara a zaben kananan hukumomi mai zuwa nan gaba.
Taron da ya samu halartar shugabannin mazabar Kujama an yi shi ne a wurin taro na otal din Goff 10 da ke unguwar Millenium City cikin garin Kaduna amma yankin karkashin karamar hukumar Chikun.
Mahalarta taro irin su Alhaji Musa Mubama Ikon Allah, ya dauki tsawon lokaci ya na ba jama’a hakuri da kuma muhimmancin haduwa wuri daya domin a samu nasarar da ake bukata, “hakika mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i na alfahari da mazabar Kujama kuma musamman yankin Millenium city da suka hada da wurare irinsu Dan bushiya da dai sauran wurare don haka a ci gaba da bayar da hadin kai da goyon baya domin nasarar ta dore”.
Mubama ya ci gaba da jan hankalin yayan APC da su shiga sako da lungunan yankunansu a rika lallashin jama’a ana ba su hakuri, a kuma rika nuna masu muhimmancin yi wa jam’iyya aiki a samu nasara domin hakan ne nasarar kowa baki daya.
“Idan aka lura a wannan yankin karkashin mazabar Kujama akwai bukatun samar da ababen more rayuwa da yawa to, idan aka samu hadin kai aka samu nasarar lashe zabe Gwamnati za ta ji dadin aiwatar mana da ayyukan da muke bukata, musamman ganin cewa Gwamnati na jin yaren a kada mata kuri’ar goyon baya a lokacin zabe”. Inji mubama.
An dai gabatar da jawabai tare da korafe korafe da dama daga yayan jam’iyya da suka hada da mataimakiyar shugaban karamar hukuma mai jiran Gado da ta bayar da hakuri ga mata da sauran al’umma inda ta roki samun hadin kan kowa, sai kuma kansilan ayyuka a karamar hukumar Chikun wanda a nan gaba idan hali ya yi za mu kawo maku dukkan yadda taro da jawaban suka gudana baki daya.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.