Home / Kasuwanci / An Yi Zanga Zangar Wutar Lantarki A Kaduna

An Yi Zanga Zangar Wutar Lantarki A Kaduna

An Yi Zanga Zangar Wutar Lantarki A Kaduna
Mustapha Imrana Abdullahi

 Mazauna rukunin gidaje na Ministerial Pilot da ke Milenium city cikin garin Kaduna sun fito kwansu da kwarkwata domin yin Zanga zangar cika masu kudin wutar da kamfanin raba wutar lantarki yake yi masu.

 

Su dai wadannan mutane sun ce suna son kamfanoni irinsu hukumar samar da wutar lantarki da Gwamnatin tarayyar Nijeriya da su tilastawa kamfanin yaba wutar lantarki na KEDCO ya daina cajin su makudan kudin wuta da yake kawo masu a halin yanzu a madadin hakan a samar masu da mitoci domin kowa ya rika sanya kati yana sanin abin da ya sha na wutarsa in kuma ba katin shi kenan mutum ba shi da wutar baki daya.

 

Masu Zanga zangar dai sun rika daga kwalaye masu dauke da sakonni daban daban kamar cewa “a Dakatar da kawo mana takardar biyan kudin wutar da ke da yawa” “mu ba kamfanoni ba ne”, inda suka ce sun fi amincewa da a Sanya masu mita kuma a shirye muke mu dauki matakin shari’a tsakaninmu da kamfanin da ke rarraba wutar lantarki.

 

Shugaban masu korafin game da batun wutar lantarkin, Abdulrauf Taha, ya shaidawa manama labarai cewa sun yi tarurruka da dama da hukumar KEDCO da NERC, amma duk da haka sai kawai su rika kawo wa jama’a wani irin takardar neman a biya su kudin wutar da ya wuce hankali da ya kama daga naira dubu 40,000 zuwa dubu dari biyu da Hamsin (250,000) a wata daya kacal.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.