Home / News / APC Ta Zamo Annoba Mai Cutarwa Ga Yan Najeriya, Inji Iyorchia Ayu

APC Ta Zamo Annoba Mai Cutarwa Ga Yan Najeriya, Inji Iyorchia Ayu

APC Ta Zamo Annoba Mai Cutarwa Ga Yan Najeriya, Inji Iyorchia Ayu
Zababben shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, a ranar Litinin ya bayyana hasashensa da cewa jam’iyyar APC karkashin jagorancin  shugaba Muhammad Buhari sun zamo wata annoba mai cutarwa ga yan kasa, abin da yake addabar kowa”.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin wadansu daga cikin yayan gamayyar jam’iyyun siyasa ta kasa (CUPP) karkashin jagorancin mai magana da yawun gamayyar kungiyar, Ikenga Ugochinyere, a gidansa da ke Abuja, ya ce barin jam’iyyar APC a Gwamnati wato a bisa madadin iko a wasu shekaru Takwas zai zamarwa Najeriya wani duhu mai tsanani.
Kamar yadda ya ce, zai iya zama wata annaba da za ta iya kasancewa ta yi jagoranci wajen ragowar Najeriya.
Ayu Ya ce, “Ni ba ni da wata jikakka tsakani na da shugaban kasa Buhari ko kuma duk mutanen da suke aiki tare da shi a fadar mulkin Najeriya. Wasu daga cikinsu ma abokai na ne misali shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Gambari.
“Ina ganin girmansa, kuma sahihin abokin ne tsawon shekaru, amma ya na cikin wata irin Gwamnati ne. Me ya sa sahihin mutum dan kasa nagari kamarsa me yake yi a can?”
Na duba cewa wannan Gwamnatin ta bata ingantacciyar rayuwar yan Najeriya Najeriya suke yi a cikin kasa musamman ta hanyar cin bashi babu kakkautawa, wanda ya ce zai iya zamarwa yan kasa musamman masu tasowa wani alakakai ko zuwa nan gaba.
Shugaban jam’iyyar mai jiran Gado ya ci gaba da cewa “Abin da Gwamnatin APC ta aikata mara kyau shi ne, misali, su na lalata ingantacciyar rayuwar yan Najeriya, su na raba kawunan yan Najeriya, su na ta cin bashi mai nauyi da ke yi wa rayuwar yan kasa barazana wanda a fili yake cewa masu zuwa nan gaba ne za su rika biyan bashin
Ba su kokarin Sanya jari da kudin da zai taimaki rayuwar yan kasa nan gaba.
“A halin da ake ciki a yanzu Najeriya na da zaman kasar da take da kudin da suka fi na kowa lalacewa a Afrika.Ka duba kasar Somaliya da ya kasance wata lalatarciyar kasa, amma ta na samun yin al’amura masu kyau fiye da Najeriya. Kudin mu sai lalacewa suke yi domin su na faruwa. Saboda mu kawai mun dogara ne da shigowa da kaya daga kasashen waje. Don haka rayuwar yan Najeriya na kara tarayyar a kullum kwanan duniya.
“Saboda haka akwai hakki a kanku ku ilmantar da yan Najeriya cewa idan har aka kara bayar da wata dama ga APC na wasu shekaru Takwas zai tabbatar da samun matsala gagaruma da za ta iya zama annoba ga kasa. Kuma hakan zai iya taimakawa wajen rabawa ko rushewar Najeriya don haka ya dace ayi dukkan mai yuwuwa a ilmantar da jama’a domin su yi amfani da dama irin ta Dimokuradiyya wajen cire wannan Gwamnati a kan karagar mulki saboda kowa ya san su babbar annoba ce da ta bayyana a fili kowa ya gani karara da ke addabar kasa a kowane irin mataki har ma da Gwamnoninsu”.
Tsohon shugaban majalisar Dattawan ya kuma yi bayani game da Gwamnan Jihar Yobe a kan irin yadda ya watsar da Jiharsa domin kawai ya rike ofishin shugaban jam’iyya na kasa wanda a kullum a halin yanzu ya na zaune ne a garin Abuja, hakan ya nuna a fili irin rashin ko’in kular da yake fama da ita a cikin APC.
Ayu ya kara da cewa  “idan la duba irin Gwamnoninsu, su ne suka fi kowa koma baya a cikin kasar. Ta yaya Gwamna zai bar Jiharsa ya koma ya tare a Abija don kawai shi ne shugaban jam’iyya na kasa. Waye me jagorantar Jihar ka? Don haka suka tabbata a matsayin masu halin ko’in kula, ba su da niyyar yi wa jama’ar da suka zabe su abin da ya dace”.
 Sai ya yi kiran samun hadin kai da sauran jam’iyyun siyasa domin a cire jam’iyyar APC daga mulkin Najeriya, ya kuma shawarci gamayyar jam’iyyun siyasa karkashin jagorancin CUPP su yi aiki da PDP kamar yadda ya ce zai zamo abun Albanu ayi aiki tare da niyyar samun ingantacciyar nasara.
Tun da farko, Ugochinyere, ya ta ya Ayu murnar zama shugaban jam’iyyar PDP sai ya yi fatan cewa hakan zai taimakawa sauran jam’iyyun siyasa musamman a zabukan  shekarar 2023.
Ya ce, “Mun yi imanin cewa da zarar an Rantsar da kai zaka taimaka wajen kara gina jam’iyyar domin kara karfafata ta yadda za a samu nasara a kowane irin mataki a zabukan shekarar 2023”.
A game da aikin juyin juya halin da gamayyar kungiyarsu ta CUPP ta yi kuwa a shekarar 2019 Ugochinyere ya gaya wa Ayu, cewa jam’iyyar PDP ta zo da kyawawan tsare tsare masu inganci da za su taimaka wajen fadakar da yan Najeriya domin a samu zabe mai inganci wanda ta dalilin wannan tsarin ne ya haifar da gamayyar jam’iyyun siyasa ta CUPP kuma mun yi yarjejeniyar da muka sanyawa hannu a cibiyar Yar’Aduwa da ke Abuja.
Ya kuma yi bayanin dalilin kawo wa shugaban ziyara, mai magana da yawun gamayyar jam’iyyun ya ce “mun zo ne domin taya ka murna zama shugaban PDP na kasa kuma dalilin da ya sa ka zama ya na da matukar muhimmanci a gare mu saboda mun san irin rawar da ka taka a can baya don haka muke bayyana ka da cewa ka na da inganci sosai wajen kara inganta tsarin Dimokuradiyya daga shekarar 1992 zuwa 1993 da ka zama shugaban majalisar Dattawa wanda kowa ya san irin tsayuwar dakan da ka yi a kan batutuwan da suka shafi Dimokuradiyya.
“Rawar da ka taka wanda hakan ya taimakawa jam’iyyar PDP ta samu nasara a shekarar 1999. Wadannan me suka Sanya muka yi imanin cewa a yanzu jam’iyyar ta fada a hannun wanda ya dace ya rike ta”, inji tawagar.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.