Home / Big News / Atiku Ya Nada Bappayo Mai taimaka Masa Na Musamman A Kan Harkar Kasuwanci A Yankin Arewa Maso Gabas.

Atiku Ya Nada Bappayo Mai taimaka Masa Na Musamman A Kan Harkar Kasuwanci A Yankin Arewa Maso Gabas.

Daga Imrana Abdullahi Kaduna
Tsohon shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin tutar jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa Atiku Abubakar ya amince da nada Dokta Ali Bappayo Adamu a matsayin mai taimaka masa na musamman a kan harkokin bunkasa kasuwanci a yankin Arewa maso Gabas.
Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar da aka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun mai bashi shawara a kan harkokin yada labarai Paul Ibe a ranar Litinin.
Nadin Bappayo, ya fara aiki ne nan take, kamar dai yadda takardar sanarwar ta bayyana, kuma hakan ya nuna cewa matasa na da gurbi a Najeriya.
Takardar da aka rabawa manema labaran ta bayyana Bappanyo a matsayin wani mutum mai kokarin inganta rayuwar al’umma musamman ma marasa karfi a cikinsu”.
An haifi Dokta Ali Bappayo Adamu, a garin Gombe a ranar 19 ga watan Maris, 1986. Ya na kuma da takardar shaidar kammala karatun digiri a kan ilimin kiwon lafiya daga jami’ar Maiduguri, ya kuma yi karatun digiri na biyu da digirin digirgir saga jami’ar Taxila da ke kasar Amurka.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa Bappayo mutum ne da ke aikin bayar da shawarar jama’a a hukumar majalisar dinkin duniya ta kasa da kasa a game da asusun kula da lafiyar yara ta ( UNICEF) kuma shi ne ya samar da cibiyar kula da harkokin bunkasa kasuwanci a yankin Arewa maso Gabas domin tafiyar Atiku ta kara kyau a shekarar 2023.
Idan za a iya tunawa wannan cibiyar kula da bunkasa harkokin kasuwanci, tuni ta tabbatar da goyon bayan ta ga Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa a 2023 mai zuwa, wannan matakin da aka dauka na sayen takardar nuna bukata da kuma takardar bayyana bukatar tsayawa takara ga PDP na Atiku Abibakar.
Wannan nadin da aka yi wa Dokta Bappayo idan za a iya tuna wa shi ne nadin da aka yi wa matashi a karo na hudu da dan takarar shugabancin kasa karkashin PDP ya yi a gabanin zaben 2023.
Dr. Bappayo’s appointment, it will be recalled also, is the fourth recent appointment of young Nigerians that the PDP presidential flag-bearer will be making ahead of the 2023 election.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.