…Mun Gamsu – Kabiru Jarumi
Daga Imrana Abdullahi
Dokta Bashir Umar Muhammad, Sakatare Janaral na tafiyar dan takarar Sanatan yankin Kaduna ta tsakiya Ambasada Shettima Usman Yerima, tafiyar da ake kira ( Capacity Movement) ya bayyana cewa sun je wajen taron da aka yi ne na dan majalisar dokokin Jihar Kaduna Auwalu Yaro mai kyau domin taya shi murna da farin cikin irin yadda yake ba dalibai damar rubuta jarabawar WAEC da NECO da nufin inganta rayuwar bil’adama.
Dokta Bashir ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a harabar wurin taron kaddamar da bayar da tallafin
Dokta Bashir ya ce kamar yadda kowa ya sani ilimi ne babbar hanyar da ke yin jagoranci wajen samun al’umma ta gari a kowace kasa, Jiha ko al’umma don haka idan ka ba su ilimi hakika ka ba su damar gina kawunansu a gaba.
” Idan aka lura da yanayin da muka samu kanmu a ciki za a ga cewa mafi yawan ɗaliban nan suna cikin iyalai ne marasa karfi da suke da rauni a tafiyar da harkokin rayuwa saboda haka wannan dama ce a gare su don haka irin wannan taimakon zai taimaka masu kwarai su samu saukin halin rayuwar da suke ciki, saboda haka muna murna da farin cikin irin wannan kokarin na Honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau”.

Da yake tofa albarkacin bakinsa tsohon shugaban karamar hukumar Kaduna ta Kudu kuma mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara a kan al’amuran Siyasa,honarabul Kabiru Yakubu Jarumi cewa ya yi
“Na halarci wannan wurin ne a matsayin wanda ke kishin Honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau kasancewarsa mutum ne mai kaunar al’umma kuma mutum ne wanda shugabancinsa na daya da na biyu duk munga abin da ya yi a kan batun kiwon lafiya, Ilimi da sauran ababen more rayuwa maza da mata tare da dattawa, hakan ya sa tun da naga za a yi wannan taron naga banga ta zama ba kamata ya yi in halarta domin ba shi ne na farko ba wadannan dalilan ne ya sa na samu karfin gwiwa in halarta domin ba matasa Maza da Mata tallafin rubuta jarabawar WAEC da NECO da kuma jarabawar JAMB”.
Kabiru Jarumi ya kara da cewa duk wadanda suka ce a mazabar dan majalisa ta Unguwar Sanusi ba Canji sun gamsu ne da irin yadda honarabul Auwalu Yaro Mai Kyau ke gudanar da jagorancin al’umma sakamakon gamsuwar da suka yi don haka muma tun da al’umma sun Gamsu babu canji muma dole mu Gamsu ba Canjin, in Allah ya yarda lallai hakika za mu bayar da dukkan gudunmawar da ya dace domin honarabul Auwalu Yaro Mai kyau ya koma a kan wannan kujerar ta dan majalisar dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Unguwar Sanusi da ikon Allah.
THESHIELD Garkuwa