Home / Kasuwanci / BA A KARA WA’ADIN CANZA KUDI BA

BA A KARA WA’ADIN CANZA KUDI BA

 

…Ranar Litinin Ba Canji
Sabanin irin yadda wadansu mutane ke yada jita – jitar cewa wai an kara lokacin canza takardun kudin da babban Bankin Najeriya bayan samun Umarnin Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari na a sauya Fasalin kudi na takardun naira dari biyu, naira Daru biyar da kuma takardar kudi ta naira dubu daya.

Jita jitar da wasu ke yadawa wai cewa an kara lokaci daga ranar Litinin din nan mai zuwa hakika maganar ba gaskiya bane domin wakilin mu ya tuntubi wata majiya mai tushe domin jin ko ya ya gaskiyar lamarin yake, kuma sun tabbatar da cewa ba a kara wani lokaci ba daga ranar Litinin mai zuwa wadancan takardun kudin da na lissafa maku za su daina aiki.
Wato dai ba wanda zai amshe su koda zaka sayo ko ka sayar duk sun bar zama takardun kudi halartattu da za a yi amfani da su.
Sai dai da wakilanmu suka zagaya cikin garin Abuja da Kaduna da kuma wasu rahotannin da muke samu a wadansu wurare na cewa jama’a sun shiga cikin rudani da firgici saboda matsalar rashin takardun sababbin kudin domin, mama’s na shan wahala a kan layin Injunan ATM domin samun sababbin takardun kudin, sai kaga Banki mai injunan ATM hudu ko sama da haka amma inji guda daya ne ko biyu ke bayar da kudin wanda hakan ke haifarwa jama’a wahala ba kadan ba domin sai wanda ya je ya gani kawai,kuma da akwai wurare da yawa da babu ma Bankunan balle a samu ATM a kusa.
Sai masu na’urar POS da yan kasuwa ke amfani da shi su kuma sun kara kudi domin a yanzu duk naira dubu Goma sai ka biya dari biyu caji kuma suma kuma a yau ranar Jima’a duk inda kaje tsofaffin kudi suke ba jama’a, saboda a duk inda muka ziyarta ba wani mai POS da yake bayar da sababbin kudin, to, ta yaya za a cimma kudirin da ake da shi na ranar Litinin?

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.