Home / News / Ba Mu Hana Kananan Hukumomi Karbar Haraji Ba – Dan Majalisa Aminu Makarfi

Ba Mu Hana Kananan Hukumomi Karbar Haraji Ba – Dan Majalisa Aminu Makarfi

Ba Mu Hana Kananan Hukumomi Karbar Haraji Ba – Dan Majalisa Aminu Makarfi

Imrana Abdullahi

Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Makarfi a majalisar dokoki ta Jihar Kaduna Alhaji Aminu Ahmad Makarfi ya Karyata jita jitar da ake yadawa cewa wai sun yi doka a majalisar dokoki sun hana kananan hukumomi karbar kudin haraji.

Aminu Ahmad Makarfi ya shaidawa manema labarai a Kaduna cewa hakika masu wannan yada jita jitar wai sun hana kananan hukumomi karbar haraji ba haka ba ne domin ba haka maganar take ba.

“Mu a majalisar dokokin Jihar Kaduna mun yi la’akari da abubuwa da dama wanda suka hada da yancin masu yin sana’a da kuma yancin duk wanda zai biya haraji sai aka yi doka guda daya kuma bai daya tak, ta karbar haraji ba wanda zai biya sabanin da yadda hukumomi daban daban na karbar haraji da suka hada da ita kanta karamar hukuma kowa ke zuwa karbar haraji ga duk wanda doka ta tanaji ya biya haraji”, inji Aminu.

Ya kara da cewa “Mu a majalisar dokoki mun yi la’akari da irin yadda ake karbar haraji a matakai daban daban kuma mun duba irin yadd shi kansa mai biyan harajin ake take masa hakki domin masu karbar harajin sun yi masa yawa sai muka gabatar da dokar cewa a samar da yadda za a karbi haraji guda daya tal a kowane mataki kuma hakan ake yi a Jihar Kaduna”.

Ya kara da cewa bayan wannan doka ta karbo wa mai biyan haraji yanci domin ya san zai biya haraji ne sau daya, ba kamar a can baya ba da masu karbar kudin harajin kananan hukumomi suzo,Gwamnati jiha da sauran masu karbar haraji duk daban daban kowa ya ce zai karbi haraji.

“Amma da wannan doka daga zarar an karbi harajin wanda kwamitin karbar haraji ne ke karba kuma mafi yawa yan kwamitin ma ma’aikata ne na kananan hukumomi. Kuma idan harajin da a misali karamar hukumar Makarfi yakamata ta karbi haraji ne to harajin zai ta fi ne ga kamfanin da aka amincewa ya karbi wannan haraji a madadin karamar hukuma, sai shi kuma ya yi lisaafin cewa ya shigarwa Jihar Kaduna harajin kaza da kaza karkashin hukumar tara haraji ta Jihar Kaduna”. Inji Dan majalisar Makarfi.

Ya tabbatarwa manema labarai cewa bayan wani lokaci sai dukkan bangarorin su zauna ayi lisaafin nawa ne suka karbo a madadin Makarfi a Makarfi in an yi lisaafin kowa za a bashi hakkinsa.

Sabanin da can sai a rika karbar haraji hawan hawa misali hukumar KASUPDA za ta iya cewa a ba su wanann, ma’aikatar ciniki da masana’antu ta jiha suma suzo, kananan hukumomi duk suzo karbar harajin, amma a yanzu sai aka mayar da shi bai daya tak karkashin hukumar tara harajin Jihar Kaduna wadda kuma ta Sanya kwamitocinta tsakanin hadin Gwiwa da kananan hukumomi da Jiha.

Saboda haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wa kananan hukumomi adalci ne, ta yi wa kananan hukumomi Gatanci ne ta yadda idan an tara kudin wakilan Gwamnatin Jihar Kaduna suzo da takardunsu na kananan hukumomi suzo da takardunsu, sai ma’aikatar kudi ta Jiha da hukumar tara harajin Jihar Kaduna duk su hanzarto kowa da nasa takardu sai ayi lissafi cewa misali karamar hukumar Makarfi kuna da kaza daga kudi na lokaci kaza da aka tara.

Wanda daman doka ta tanadar cewa nawa ne za a fitar na hidimar tara kudin harajin kuma nawa ne kudin karamar hukuma, sai Gwamnatin Jihar Kaduna ta mayar wa da suke na karamar hukuma kaza ne bisa tsarin mulkin Nijeriya.

Da yake bayanin ko nawa ne yadda ake kason kudin sai ya ce kamar kudin da ake tarawa a kasuwa da Tashoshin mota kaso sittin cikin dari na kananan  hukumomi ne, Kawhi Arba’in kuma hukumar tara haraji da kuma kamfanoni da aka sa tara harajin da kudin alawus alawus na wadanda aka sa suke duba wannan harkokin tara kudin.

Kuma idan karamar hukuma za ta biyo sawun kudinta a duk wata wata ne ko sai bayan wata uku uku ne ya rage gareta kowa dai ya na da nasa lisaafin da takardunsu na kudin da aka tara sai suje hukumar tara haraji sannan a biyasu abin da ya zamanto wajibi ne na ta daga karshe.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.