Home / Labarai / Yan Sanda Sun Bindige Yan Bindiga Uku, A Katsina

Yan Sanda Sun Bindige Yan Bindiga Uku, A Katsina

Yan Sanda Sun Bindige Yan Bindiga Uku, A Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Rundunar yan sandan Jihar Katsina karkashin jagorancin jajirtaccen kwamishinan yan Sanda Sanusi Buba sun samu nasarar bindige wadansu yan bindiga guda uku har lahira.

 

Su dai wadannan yan bindigan sun addabi al’ummar karamar hukumar Dutsinma da kuma karamar hukumar Dan Musa da ayyukan ta’addanci.

 

Kwamishinan yan sands Sanusi Buba ya bayyana hakan a lokacin da yake nunawa manema labarai Gawar mutanem uku tare da makamansu.

 

Ya ci gaba da cewa ofishin jami’an yan Sanda na kasa ne da ke Dutainma suka fafata da yan bindigan bayan sun samu waya daga wadansu mutane game da yan bindigar da suke yi wa yankunan ta’addanci, kuma cikin ikon Allah jami’an tsaron suka samu nasara a kan miyagun.

 

“Su dai wadannan yan bindiga da suka kai 50 sun kaiwa wani kauye unguwar Bera da Mangoro da ke Dutsinma hari ne”.

 

Kwamishinan ya kara da cewa nan da nan jami’an yan sandan suka bi sawun yan bindigan a kusa da kauyen Mara zuwa Tashar Gajere inda suka samu nasarar halaka yan ta’addan guda uku a cikinsu.

 

Ya kara da cewa yan bindigar uku da aka halakar an same su da bindigogi kirar AK47 huda biyu da albarusai guda 15 masu milimita 7.62.

 

Kwamishina Buba ya kuma ce an Sanya jami’an tsaro a yanzu haka da za su gudanar da bincike domin samo sauran yan ta’addan da suka shiga daji da raunuka a jikinsu a kuma samo makamansu.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.