Home / Big News / BA MU KARBI KUDI NAIRA MILIYAN 640 BA – JAM’IYYAR LEBO TA KADUNA

BA MU KARBI KUDI NAIRA MILIYAN 640 BA – JAM’IYYAR LEBO TA KADUNA

Daga Imrana Abdullahi

Jam’iyyar Lebo reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin Auwal Ali Tafoki sun bayyana rashin jin dadinsu game da batun zargin karbar kudin tallafi da karo – karo da nufin samun nasarar zaben 2023 a Jihar Kaduna.

Alhaji Auwal Ali Tafoki wanda shugaban jam’iyyar APC ne a Jihar Kaduna ya bayyana rashin jin dadinsu ne a wajen wani taron manema labarai da suka yi a ofishin jam’iyyar na Jiha.

Inda ya ce hakika batun karbar kudi naira miliyan sama da dari 640 wani al’amari ne da ba su ji dadinsa ba ko kadan domin ana kokarin shafawa jam’iyya tare da dan takarar ta kashin kaji ne kawai.

“Saboda haka ne mu a jam’iyyar Lebo matakin Jihar Kaduna muke kokawa domin lamarin ya ba ta mana rai kwarai”.

A yau muke yi maku bayanin cewa akwai wata takardar da ke yawo a kafafen Sada zuminta mai dauke da kwanan wata 17 ha watan Afrilu, 2023 da ta fito daga wani kamfanin lauyanci da ake kira Vax Justicae Attoney ( Aniah A. Ikwiem & Associate) da adireshin Abuja a madadin Iniiniya Mike Auta da jam’iyyar Lebo ta Jihar Kaduna.

  Takardar an mika ta ne kai tsaye ga dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a zaben shekarar 2023 karkashin jam’iyyar Lebo Honarabul Jonathan Asake.

Takardar da ta zamo ta yadu a yanar Gizo musamman a kafafen Sada zumuntar yanar Gizo an ambaci jam’iyyar Lebo da Inj8niya Mike Auta suna kalubalantar Honarabul Jonathan Asake

game da batun laifin karbar kudi naira sama da miliyan dari 640, suna cewa kudin da aka samu ne daga wadanda suka bayar da taimako tallafi da karo – karon kudi da nufin a taimakawa jam’iyyar ta samu nasarar lashe zaben 2023

Bayan muna fama da wani babban kalubale daga can sama a mataki na kasa, sai kuma,kawai muka samu wannan sako ta kafafen Sada zumunta na yanar Gizo na zamani daga wannan kamfanin lauyanci da muka ambata a can baya.

Bayan mun karanta wannan takardar da abin da ta kunsa sai muka fahimci cewa an hada har da jam’iyyar Lebo a cikin batun, saboda haka bayan mun yi tuntuba sosai a game da lamarin sai muka yanke hukuncin cewa gara mu fayyace komai domin a fahimci lamarin sosai da sosai.

1. Mufa ba wai shugabannin jam’iyya ba ne kawai na Jiha, muna cikin gudanar da harkokin ta ka’in da na’in, wato jam’iyyar Lebo.

  2) Don haka mun barranta da wannan takarda, kamfanin lauyanci da Iniiniya Mike Auta a game da wannan batu a matsayin mu na jam’iyyar Lebo a Jihar Kaduna ba mu ta wata tantama ko shakkun cewa babu wasu makudan kudaden da suka shigo mana da suka kai wannan makudai daga kowane mutum.

 3)  Shi wannan kamfanin Lauyanci da Injiniya Mike Auta ba su tuntube mu ba game da wannan batu ko kuma kowa ne irin batu ma da ke da dangantaka da wannan

3. Saboda haka hakika mun yi mamakin faruwar hakan domin mun ji lamarin ya zamo bambarakwai don ba mu san wani lamarin Barnar kudi kamar wannan ba kuma har yanzu babu wani koken da aka gabatar mana

4) Hakika mun kadu mun kuma ji wani iri da har wannan irin magana aka fitar da ita a yanar Gizo musamman a dandalin Sada zumunta duk da irin bayanan da take dauke da su, amma sai dai muka jita can a wani wuri kawai.

A saboda haka mu, a jam’iyyar Lebo reshen Jihar Kaduna muna bukatar wannan ba da ba ta lokaci ba.

1.A fito fili a nemi Gafara daga kamfanin lauyanci da kuma shi kansa Injiniya Mike Auta da ya bayar da umarnin cewa ya hada da mu, muna son ayi wannan neman Gafara ne a kafafen Sada Zumunta, jaridun da ake bugawa da kuma kafafen rediyo.

2) A fito fili ayi mana bayanin yadda abin yake tare da misanta mu da wannan batu baki daya a cikin kwanaki Bakwai daga yau.

4) Kuma bayanin da za yi muna son a wallafa shi a cikin wasu manyan jaridu na kasa, kafafen Sada zumunta da kuma kafafen gidajen rediyo

5) Idan kuma aka kasa cika wannan to, ba abin da zamu yi sai dai mu dauki matakin shari’a kawai mu kare martaba da mutuncin jam’iyya kuma mu nemi diyya sakamakon matsalar da takardar ta haifar.

6) Kuma za a kafa kwamitin da zai binciki wanann batun da nufin manufar hakan.

7) Kuma kwamitin zai gano irin rawar da wasu suka taka wadanda za su iya kasancewa yan jam’iyya ne.

8)Duk iron abin da kwamitin ya gano zai taimaka mana wajen sanin matakin da za mu dauka a kan duk wani memban jam’iyya da ya kasance mai kunnen kashi da har aka danganta mu da batun da ba mu da masaniya a kansa.

Muna kuma yin amfani da wannan damar domin tabbatarwa da duniya cewa babu wani dan jam’iyya da ya fi karfin dokar jam’iyya

Muna kuma shaida wa yayan jam’iyyar mu da masu goyon bayan ta cewa kamar kowa ce jam’iyya ba za mu zauna ba tare da kalubale ba don haka kada kowa ya girgiza ko jin wani shakku a cikin zuciyarsa domin hakan ba zai yi mana komai ba sai ma Santa mu kara bunkasa kawai

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.