Home / Labarai / Ba Mu San An Kori Kowa Aiki Ba – Ishaku Yakubu

Ba Mu San An Kori Kowa Aiki Ba – Ishaku Yakubu

Ba Mu San An Kori Kowa Aiki Ba – Ishaku Yakubu
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar ma’aikatan Jinya da unguwar tsoma ta kasa reshen Jihar Kaduna Ishaku Yakubu, ya bayyanawa manema labarai a Kaduna cewa su a matsayinsu na masu aikin Jinya da  unguwar tsoma a Jihar Kaduna da suka kai a kalla mutane dubu 2500 ba su ma san wai an Sallami wadansu daga cikin yayansu aiki ba.
Ishaku Yakubu ya shaidawa manema labarai hakan ne a Kaduna, inda ya ce su a matsayinsu ba su na rokon wani ya daukesu aiki ba ne,”neman my ake yi a wadansu jihohi a duk fadin Nijeriya, amma wadanda suke wannan aikin su a matsayinsu na shugabanni kullum su na kokarin ba abokan aikinsu ne hakuri su zauna a Kaduna domin Jiharsu ce za su yi wa aiki su taimakawa yan jiharsu, domin ana nemansu a ko’ina ciki har da wajen Nijeriya”, inji Ishaku.
Ishaku Yakubu ya ci gaba da cewa ba a cikin gidan rediyo ko Talbijin aka dauke su aiki ba akwai hanyoyin da aka bi aka dauke su aikin don haka sai an bi tsarin yadda ya dace idan ana son sallamar ma’aikaci irinsu da ke da matukar muhimmanci a wajen kula da lafiyar al’ummar kasa baki daya”.
Abubuwa uku na shaidawa shugabannin asibitin Barau Dikko da suka kira ni taro a ranar Litinin da ta gabata na farko “na gaya masu cewa ba aikin yayan kungiyar da nake yi wa shugabanci ba ne su kulle Kofar shiga asibiti, wannan sai wadanda aka dauka aikin Gadi, na biyu na gaya masu cewa ba aikin yayan kungiya ta ba ne su Sallami duk wani majinyaci da ya je asibiti neman a lafiyarsa, sai kuma na uku cewa ba gaskiya ba ne wata ma’aikaciyar jinya ta cirewa wani yaro na’urar taimaka masa ya yi numfashi wannan ba gaskiya ba ne ko kadan”, inji Ishaku.
“A lokacin da muka samu wannan labarin cewa an cirewa yaro na’urar da ke taimaka masa yin numfashi mun kafa bincike domin tabbatar da gaskiya inda muka bi iyayen yaron har asibitin da suka kai shi sakamakon yajin aikin da aka fara, mun kuma he asibitin har wasu yan jarida sun tattauna da uwar yaron ya na nan da ransa kuma ta fadi gaskiyar lamari wanda ya zuwa yanzu haka yaron nan na nan da ransa kuma har iyayensa sun dawo da shi asibitin Barau Dikko domin ci gaba da nema masa lafiya, to Gawa ce aka dawo da ita kome? don haka ba wanda ya Isa ya bata mana suna kuma za mu nemi hakkin mu a game da wannan maganar.
“Masu yin aiki irin na mu ana neman mu ne a ko’ina cikin duniya kowace rana masu aikin jinya da unguwar Zoma na ficewa daga Nijeriya zuwa wadansu kasashe ana kuma daukarsu aiki da makudan kudi masu tsoka, haka abin yake a wasu Jihohin Nijeriya ana daukarsu aiki cikin daraja da mutunci ba kamar yadda ake neman jama’a da sharri ba duk da irin aikin da suke yi”, inji Ishaku.
Ya kara da jaddada cewa sun shirya neman Hakkinsu na kokarin bata masu su na a matsayinsu na yayan kungiyar masu aikin jinya da unguwar Zoma a duk fadin Jihar Kaduna da ya hada da dukkan kananan hukumomi 23, da muke da mambobi dubu 2500 da suke kula wa da lafiyar jama’a.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.