Home / KUNGIYOYI / An Yaudare Mu Ne – wadansu Mata

An Yaudare Mu Ne – wadansu Mata

An Yaudare Mu Ne – wadansu Mata

Mustapha Imrana Abdullahi
Wadansu tarin mata da aka kwaso domin su kalubalanci gangamin yayan kungiyar kwadago ta kasa da take yi a Jihar Kaduna sun bayyanawa jami’an tsaro cewa yaudararsu aka yi da nufin za a yi taron siyasa ne, amma sai da aka kawo su kan marabar titin Golf course da hedikwatar yan Sanda ta kasa da ke Kaduna sai suka ga ne cewa ba gaskiya ba ne abin da ake gaya masu.
Dimbin tarin matan sun tabbatarwa da gangamin yan kungiyar kwadagon ne lokacin da suka tunkare su domin jin me yakawo su wajen taron yan kwadago.
Wadansu daga cikin yayan kungiyar masu yin gangamin sun tambayesu cewa ku da kuke mata sanye da hijabi me kuka zo yi nan? hakika kun ba mu kunya da muka ganku a haka”, inji yan kwadago.
” Nan da nan sai wasu daga cikinsu suka ce an kwaso su ne da sunan wai za a yi taron siyasa, amma da suka zo wannan wuri sai suka ga ba haka ba ne yaudararsu aka yi da cewa za a yi taro kuma su ba su ga hakan ba domin abin da suka tarar wani abu daban ne, mu ba za mu tunkari taron jama’a mai yawa  irin wannan ba da sunan gangamin goyon bayan wani ko wasu ba don haka mun yi nadamar zuwa wannan wuri har ga Allah saboda yaudara mu aka yi”, inji mata.
Ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin dai daukacin matan sun sulale daga wurin taron inda kowace ta kama gabanta.
Kuma kwamishinan rundunar yan Sanda ta kasa reshen Jihar kaduna ya samu zuwa Kofar ofishin yan kwadago na kasa reshen Jihar Kaduna inda ya tattauna da manema labarai.
Inda kwamishinan rundunar Yan Sandan ya shaidawa manema labarai cewa ya fito ne ya na zagayawa domin ya tabbatar da komai na tafiya ba tare da samun wata matsala ba.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin biyu na yayan kungiyar kwadago da Gwamnati  da su gujewa yin abin da bai dace ba.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.