Home / News / BA ZAN YAUDARE KU BA – SULEIMAN SHINKAFI

BA ZAN YAUDARE KU BA – SULEIMAN SHINKAFI

….Daga Zuwan Suleiman Shu’aibu Shinkafi APC Ta Canza Baki Daya – Jam’iyyar APC
IMRANA ABDULLAHI Daga Shinkafi
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya yi kira ga daukacin yayan jam’iyyar APC da su bashi hadin kai da goyon baya domin al’amura su gyaru a karamar hukumar Shinkafi.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Shinkafi, a ziyararsa gidan shugaban APC na karamar hukumar Shinkafi Alhaji Halilu Bama.
“Ni fa ina tabbatar maku cewa kare mutuncin yayan APC da al’ummar Karamar hukumar Shinkafi, domin ruwa za a yi kowa ya jika”.
“Tun da farko ku Sani ba zan yi wa jam’iyya kwange ba, kuma ina son ku Sani ba zan Yaudare ku ba ko kadan, buri na inganta rayuwar jama’a kamar yadda na saba ina aikata wa”.
Tallafawa yayan jam’iyya ya zama wajibi a gare ni, domin ba za mu ba mai girma Gwamna kunya ba.
” ina son kowa ya Sani cewa Gwamna Jihar Zamfara Dokta Bello Muhammad Matawalle na bayar da kudi ga kowace karamar hukuma wanda sakamakon hakan a kwanan baya har sai da Gwamna ya saya wa kowa ne Kantoma mota irin ta alfarma domin tabbatar da martabar da kowa ne Kantoma ke da shi kuma a samu dadin tafiyar da jagorancin jama’a”.
Na taba zuwa nan daga ni sai 406 amma domin yan Shinkafi na sayar da ita na koma gida a motar haya, kasancewar su wadanda hadari ya rutsa da su duk na biya kudin maganin da za a yi masu wasu a asibitin Kano wasu a asibitin Sakkwato don kawai su samu lafiya.
“Ba abin kunya ga kantoma ya bar exco ba komai ko rigar kirki babu, wannan babu sam, Zan rika samowa karamar hukuma tallafi domin a Tallafawa jama’a
“Zan iya samo rance bayan nan ni a daure ni, don haka babu wanda zai nemi wani abu ya rasa”.
Za mu yi shugabanci irin na Bama, idan an bashi zai kara da nashi abin hannun saboda inganta rayuwar jama’a.
“Ni kadai Gwamna yaje ofishina domin ya gani abin da kake yi,saboda Gwamnan na son ya ganewa idanunsa kome ake ciki tun da kullum sai ya ga dimbin jama’a wurin ofishina”.
Sani Dan Bara Garkuwan Shanawa mataimakin shugaban APC na Shinkafi, ni fa mun yi tafiya tare da shi a can baya “ina tabbatar maku duk abin da yake fadi gaskiya ne domin na san hakan.
Dan Madamin Shinkafi Aliyu Dan Madami, ina son ku san idan zaku yi hulda da mutum ku san da wa zaku yi hulda, shi dan asalin Shinkafi ne domin nan ne asalin babansa.
“Kowa ya Sani daga zuwanka Shinkafi jam’iyyar APC ta Farfado domin kowa ya shaida hakan.
“Muna yin kira ga Gwamna da ya saurari dukkan abin da aka yi a taron da aka yi domin a tabbatar da an yi aiki da abin da jama’a ke so, jam’iyya ta ci gaba da bunkasa
Shugaban jam’iyyar APC Alhaji Halilu Bama, muna fatan duk abin da za mu tattauna ya amfana.
Kasuwar da ke da kyau tun daga ranar Laraba ake gane ta “hakika muna farin cikin irin abubuwan da Suleiman Shinkafi ya kawo.
An fitar da tsare tsare inda za a dauki mutane dari uku, domin yin tsarin da kowa zai amfana.
Wannan dan takara ya na yi ne domin mutane kamar yadda komai ya tabbatar Dokta Suleiman Shinkafi, na zuwa ya nemo abin duniya jama’a su amfana.

About andiya

Check Also

Union Across River Niger: New Nigerian Editor Brother’s Wedding Grounds Makurdi

    Makurdi the capital of Benue State was agog all through the weekend, as …

Leave a Reply

Your email address will not be published.