Babban Hafsan Sojojin kasa na Najeriya Janar Christopher Gwabin Musa ya shawarci masu yin wa’azi a Najeriya da su rika yin kira ga zaman lafiya a lokacin wa’azinsu a cikin Cocina da kuma dukkan shirye shiryen da suke Gabatarwa jama’a.
Shugaban sojojin ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya kai wata ziyara hedikwatar kungiyar Kiristoci ta kasa CAN da ke babban birnin tarayya Abuja.
Shugaban sojojin ya ce ziyarar na da nufin samar da wata kyakkyawar dangantaka ne tsakanin sojoji da shugabannin addini domin fadakarwa a kan batun zaman lafiya da hadin kai ta yadda za a samu ci gaba da bunkasar kasa baki daya.
Janaral Musa ya ci gaba da bayanin cewa ya na yin kira ga kungiyar da su ci gaba da yi wa sojoji addu’a domin samun nasara game da ayyukan da ke gabansu,muswmman ma a wannan mawuyacin lokaci da ake ganin akwai ayyukan yan bindiga, batagari da dai sauran ayyukan masu aikata laifi iri iri da ke yin barazana wajen samar da zaman lafiya da tattalin arzikin kasa.
A yayin da yake nuna farin ciki ga babban Hafsan sojojin da ya kai wa shugaban kungiyar kiristocin ziyara, Bishof Daniel Okor, cewa ya yi kungiyar Kiristoci ta CAN a koda yaushe ta na bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga sojoji a dukkan fannoni baki daya.
Bishof din ya kuma ce a koda yaushe kungiyar ba za ta yi kasa a Gwiwa ba wajen bijirowa da shawarwarin da za su kara karfafa kyakkyawar dangantaka da dukkan rundunonin soja baki daya da hakan zai kara samar da zaman lafiya da hadin kai a kasa da kuma har ma da tsakanin kungiyoyin addinai a Najeriya.
Indai za a iya tunawa babban Hafsan sojojin na Najeriya Janar Christopher Musa Gwabin a kasa da sati daya ya kai ziyara babban masallacin Abuja inda ya gana da shugabannin majalisar koli na harkokin addinin musulunci duk da nufin samar da kyakkyawar dangantaka, Zaman lafiya da hadin kai tare da tsaro a Najeriya.