Home / News / Bamu Tsayar Da Dan takara Ba – Auwalu Branko

Bamu Tsayar Da Dan takara Ba – Auwalu Branko

Bamu Tsayar Da Dan takara Ba – Auwalu Branko
Imrana Abdullahi
Shugaban jam’iyyar PDP reshen karamar hukumar Kaduna ta Arewa cikin Jihar Kaduna Alhaji Auwalu Branko ya karta jita jitar da ake yadawa cewa wai tuni sun tsayar da Dan takarar da zai yi wa jam’iyyar takara .
Alhaji Auwalu Branko ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi tawagar daya daga cikin yan takarar kujerar shugabancin karamar hukumar karkashin PDP honarabul Balarabe Isa Abdullahi Kwankwasiyya tare da dimbin tawagarsa da suka je ofishin karamar hukumar da ke kan titin Junction cikin garin Kaduna.
Auwalu Branko wanda a lokacin da ya tarbi tawagar dan takarar lokacin yana tare da dukkan shugabannin jam’iyyar a matakin karamar hukumar Kaduna ta Arewa ya tabbatar wa da duniya cewa duk masu yada irin wannan magana su na fadin abin da ba gaskiya ba ne.
“Mu ba mu tsayar da kowa takara ba saboda yin hakan ba tsarin jam’iyya ba ne don haka babu irin wannan a cikin tsarin mu ko kadan, muna tabbatarwa da dukkan yan takara cewa za mu yi wa kowa adalci”, inji shugaban PDP.
Ya kara da cewa muna jin dadin irin yadda ake motsa jam’iyya domin muna da labarin irin yadda ake gudanar da al’amura a koda yaushe, kuma hakika muna godiya da hakan.
“Muna son a rika gudanar da duk al’amura a cikin tsari ta yadda za a fahimtar Juna domin nasara a gar mu take da ikon Allah”.
Da yake tofa albarkacin bakinsa dan takarar kujerar shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa karkashin tutar jam’iyyar PDP honarabul Balarabe Isa Abdullahi Kwankwasiyya cewa ya yi dalilin da ya sa yazo tare da jama’arsa shi ne domin ya kawowa shugabannin jam’iyyar na Kaduna ta Arewa a rubuce bukatarsa ta tsayawa takara.
Inda ya ce “in ya zama shugaban karamar hukumar Kaduna ta Arewa ba zai bari son zuciya ko mancewa da al’umma ba, San tabbatar da tsare gaskiya da Amana domin a samu ci gaba”.
Ya kuma yi wa daukacin shugabannin jam’iyyar bisa irin yadda suke karbarsa a koda yaushe, wanda hakan na kara karfafa masa Gwiwa wajen fitowa neman wannan kujera a matsayinsa na dan asalin Jihar Kaduna mai yancin ya nemi duk takarar da ya ga zai iya.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.