Home / Kasuwanci / Ga Yadda Farashin Amfanin Gona Yake A Kasuwar Giwa, Funtuwa Da Dandume Jihar Katsina

Ga Yadda Farashin Amfanin Gona Yake A Kasuwar Giwa, Funtuwa Da Dandume Jihar Katsina

Ga Yadda Farashin Amfanin Gona Yake A Kasuwar Dandume Jihar Katsina
Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar yadda wata tawagar wakilan mu karkashin jagorancin M Imrana Abdullahi lokacin da suka ziyarci kasuwar domin bincikar yadda ake sayar da Buhunan amfanin Gona, kasancewar karamar hukumar Dandume na cikin sahun gaba a wajen sanarwa Nijeriya abinci ta hanyar Noma.
Ga dai irin yadda Buhunan amfanin Gonar yake:
Masara Dubu 18,000
Dawa Dubu 17,000 ko 17 ba naira dari uku.
Farin Wake Dubu 32,000
Waken Soya Dubu 18,500
Ga dai yadda farashin amfanin Gona ya kasance a Jiya Lahadi a kasuwar Giwa cikin Jihar Kaduna, kamar yadda Malam Abdullahi Mai sana’ar sayar da Buhunan hatsi ya shaida mana.
Buhun Dawa 17, 200
Masara Dubu 18,200
Farin Wake Dubu  32,000
Waken Soya Dubu 27,500
Sai kuma a yau ranar Litinin 1 ha watan Mayu, 2021. A kasuwar Funtuwa cikin Jihar Katsina daya daga cikin yankin da ke ciyar da Nijeriya har da kasashen ketare da abinci, farashin kayan amfanin Gona ya kai kamar haka: kamar yadda Malam Kabiru mai sana’ar sayar da Buhunan hatsi ya shaida mana.
Dawa buhu daya ana samun na Dubu 17, 500, sai 17,200 ko da dari uku ya danganta da kyau da kuma cikar buhu
Sai Masara Dubu 18, 500
Farin Wake Dubu 35,000, 31,000 da kuma 31,000 ya dai danganta da kyawun kaya da cikar buhu.
Waken Soya buhu Dubu 28, 500
Bisa ga wannan mun samu cewa farashi ya fi dagawa a kasuwar Funtuwa
Za mu ci gaba da kawo maku irin yadda farashin yake a wasu kasuwanni

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.