Home / News / BAN TABA GANIN ZABE MAI KYAU BA KAMAR WANNAN – USAMAN NASARAWAN MAI LAYI

BAN TABA GANIN ZABE MAI KYAU BA KAMAR WANNAN – USAMAN NASARAWAN MAI LAYI

Daga IMRANA ABDULLAHI

ALHAJI Usman Abdullahi Nasarawan Mai layi, babban mataimaki ne na musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara ya bayyana cewa tun da yake bai ta ba ganin kyakkyawan zaben da aka yi kamar wannan karon ba.

Usman Abdullahi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Gusau fadar Gwamnatin Jihar Zamfara.

Usaman, ya ce hakika an yi kokari yin zaben da ya gudana domin an yi zabe babu kudi amma jama’a sun zabi abin da suke bukata kuma duk wanda ya ci zaben nan kuri’ar jama’a ce ta bashi zaben domin ba sayen kowa ya yi da kudi ba.

A game da zaben Gwamna kuwa Usman Nasarawan Mai Layi ya ci gaba da cewa, kasancewar duk wanda zai yi zabe ya na yin addu’ar Allah ya zabar masa abin da ya fi zama alkairi kuma an Jefa kuri’ar Allah kuma ya tabbatar da abin da ya fi zama alkairi.

“An yi zabe ba tsangwama ba magudi ba kuma wanda aka sayi kuri’arsa domin ba ko Kwabo an yi zabe mutane sun zabi abin da suke bukata an kuma bar hukunci daga Allah.

” A halin yanzu na shekara 60 zuwa 65 tun da na tashi ina siyasa, ban ta ba ganin zabe mai kyau ba irin wannan zaben da aka yi a kwanan nan, saboda ko a Amurka ta samu zabe irin haka to an yi zabe mai kyau domin an kamanta kuma duk wanda aka zaba Allah ne ya bashi kujerar nan ba tare da wani makudi ba domin ba hanyar yin magudin an yi zabe na tsakani da Allah kuma mun Karbe shi da hannu biyu. Muna fatan Alkairan da ke ciki Allah ya kawo mana su kuma idan da matsaloli Allah ya kawar mana su a ciki”.

Usaman, babban mataimaki na Gwamnan Zamfara ya kara da cewa shi a ganinsu zaben Gwamnan Jihar Zamfara da za a yi kamar yin karashe ne kawai, kamar a fara Shara ne a dan rage yar tuntuba sai kawai a karasa cirewa domin kowa ne irin mutum a yanzu jiraye yake yazo ya yi zabe na Gwamna Matawalle. Wannan jam’iyya ta APC Allah yasa mata kwarjini ga jama’a kamar yadda mu muka Sani ne Gwamna Matawalle duk yadda ake yi hakika ya na yin iyakar kokarinsa ga jama’a kuma Allah yakamasa da alkairi”.

“Tun da nake a cikin harkokin siyasa ba a taba samun wani Gwamnan da ya taimakawa mutane da hanyoyin da za su ci abinci ba kamar wannan mutum Gwamnan Zamfara Matawalle saboda ya dauki mutane fiye da dubu Ashirin tsakanin S A da SSA mukamai da ban daban duk an taimaka masu yadda za su ci abinci kuma su matso da jama’a kusa da Gwamnati. An hana su da zaman banza ko yin turowe wato ( bangar siyasa) kaga an taimaki mutane fiye da zato ya taimaki al’umma. Kuma jama’a a shirye suke su taimake shi don haka in Allah ya yi a ranar zabe sai an samu kuri’ar da ta wadda aka samu a wannan zaben da ya gabata sai ta lunka ta lunka ta lunka in Allah yaso.

About andiya

Check Also

Zulum meets Tinubu over South Chad Irrigation Scheme

  .. Says Tinubu approves Gwoza FCE take off     Borno State Governor, Babagana …

Leave a Reply

Your email address will not be published.