Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai barin gado, a ranar Juma’a ya kai wa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu a wani rangadin sanin makamar aiki a fadar shugaban kasa da ke Abuja, wanda hakan zai ba sabon zababben shugaban mai jiran rantsuwa sanin yadda fadar take.
Buhari da Tinubu sun isa dakin taron manema labarai da misalin karfe 1:18 na rana jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a a masallacin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Inda shugaban mai barin Gado ya ce “Wannan ita ce Taswirar inda za ku gana da ‘yan jarida,” Buhari ya shaida wa Tinubu yayin da mutanen biyu suka fito daga dakin jira na fadar shugaban tarayyar Najeriya”.
Wannan dai na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da shugaban kasar ya bai wa Tinubu lambar girmamawa ta kasa ta Babban Kwamandan Tarayyar Najeriya da kuma Babban Kwamandan da kuma wata babbar lamba ga zababben mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, a wani dakin taro na da yake fadar ta shugaban kasa duk a jiya.
A ranar Alhamis ne mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kai wa Shettima ziyara har suka yi rangadi a fadar shugaban kasa.
Shugabannin biyu sun yi musayar takardu gabanin mika mulki a hukumance a ranar Litinin, 29 ga Mayu, 2023.