Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Cibiyar da ke rajin Tallafawa manoma ta kasa mai suna “National Agricultural Mechanization Co operative Society” karkashin jagoranci Dan marayan Zaki Dokta Aliyu Muhammad Waziri na gayyatar daukacin al’umma zuwa wajen gagarumin taron kaddamar da Ko- odinetocinta 44 na Jihar Kano.
Tare da wayar wa da jama’a kai a kan tallafin da Gwamnatin tarayya za ta ba kaso Tamanin (80) cikin dari na mata da kuma Maza a kan kiwon Kaji da karin haske a kan Noman zamani.
Za a yi taron ne a ranar Talata 2 ga watan Nuwamba 2021 a wurin taro na dakin karatu na Jihar Kano da misalin karfe 11 na safe da ke kan titin Ahmadu Bello cikin garin Kano.
Babban Bako mai girma Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje, mai kaddamarwa mataimakin Gwamnan Kano kwamishinan ma’aikatar Gona Dokta Nasiru Yusuf Gawuna
Uban taro shugaban manoman zamani na kasa Honarabul Dokta Aliyu Muhammad Waziri
Mai masaukin Baki shugaban cibiyar na Jihar Kano Andulhamid Yakubu.
Allah ya bada ikon zuwa amin