Home / News / Ciyo Bashi: Yan Majalisa Sun Gamsu Da Hujjojin Tinubu – Sanata Rufa’I Hanga

Ciyo Bashi: Yan Majalisa Sun Gamsu Da Hujjojin Tinubu – Sanata Rufa’I Hanga

Daga Bashir Bello, Abuja.
Senator, Rufai Hanga ya tabbatar da cewa yan Majalisar tarayya  sun amince da hujjojin da gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu ta gabatar wa majalisar  na ciyo bashin Kudi Dalar Amurka Biliyan 7.8 da kuma kudin tarayyar Turai na Yuro miliyan 100 a satin da ya gabata.
Dan Majalisar  Mai wakiltar Kano ta tsakiya Sanata Rufa’I Sani Hanga ya tabbatar da hakan ga manema labarai ne a ofishinsa da ke harabar majalisar kasa a  Abuja.
Hanga ya ce Majalisar ta yi nazari a kan  hujjojin da Shugaban Kasa ya gabatar mata na dalilansa na ciyo bashin kuma sun gamsu da dukka hujjojin sabo da haka ne suka amince da a ciyo bashin.
Dan Majalisar ya ce sun kulle kofa isu –  isu kawai kuma sun gamsar da kansu sannan sun yi alkawarin ganin cewa idan an ciyo bashin za su saka ido wajen ganin an aiwatar da duk abubuwan da aka ce za ayi da kudin da aka karbo bashin domin aikata wa.
Sanata Hanga ya kara da cewa “ kowace kasa ta duniya ta na cin bashi. Kasashe irin su Amurka da Ingila da sauransu suma suna cin bashi. Ko Aliko Dangote ma wanda ya fi kowa kudi a Afirka shi ma yana cin bashi. Abun dubawa a nan shi ne idan an ciyo bashin me za ayi da shi? Idan abu mai kyau ne za ayi da shi lallai ba matsala”, inji Sanata Hanga.

About andiya

Check Also

Northern govs meet in Kaduna, design regional economy, human capacity devt

    The chairman, Northern States Governors’ Forum (NSGF), Muhammadu Inuwa Yahaya, has called for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.