Home / News / Cutar Korona: An Rufe Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

Cutar Korona: An Rufe Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

 Imrana Abdullahi
Sakamakon samun wani dan majalisar dokokin Jihar Kaduna da aka yi dauke da cutar Korona a yanzu an rufe majalisar.
Wannan lamarin dai ya biyo bayan irin yadda aka tabbatar da cewa daya daga cikin yan majalisar dokokin ya kamu da cutar ne.
An dai bayyana rufe majalisar ne biyo bayan irin yadda aka gayyaci wadansu yan majalisa Takwas domin yi wa kwamitin Da’a na majalisar bayanin abin da suka Sani a kan irin hargitsin da ya tashi a majalisar a kwanan baya, wanda aka ga yan majalisar a faifan bidiyo suna ba hammata Iska
Hargitsin dai ya zo ne lokacin da aka cire mataimakin shugaban majalisar Dan majalisa Muktar Isa Hazo.
An dai rufe majalisar ne domin daukar matakin bincike da kuma yin maganin cutar Korona da ke durkusar da tattalin arziki da kuma al’amuran duniya baki daya.
A halin yanzu dai majalisar dokokin Jihar Kaduna na karkashin jagorancin dan Majalisa Yisuf I Zailani ne mai wakiltar mazabar Igabi ta Yamma.

About andiya

Check Also

STRINGENT MEASURES AGAINST HUMAN TRAFFICKING AND GENDER BASED VIOLENCE IS THE ONLY SOLUTION – MATAWALLE

Zamfara State Executive Governor, Hon.Dr. Bello Mohammed Matawalle MON (Shattiman Sakkwato) has called for more …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *