Home / News / Rashin Shgabanci Ne Ya Kawo Yamutsi A Majalisar Dokokin Jihar Kaduna – Mamadi

Rashin Shgabanci Ne Ya Kawo Yamutsi A Majalisar Dokokin Jihar Kaduna – Mamadi

Imrana Abdullahi
Wani Jigon jam’iyyar APC a Jihar Kaduna tsohon dan majalisar wakilai ta kasa Alhaji Muhammad Abubakar Mamadi, ya bayyana cewa rashin ingantaccen shugabanci ne ya haifar da matsalar tashin tashinar da ta faru a majalisar dokokin Jihar Kaduna.
Alhaji Abubakar Mamadi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a kaduna, inda ya ce ta yaya wani wanda ba dan majalisa ba zai shiga har cikin majalisa ya haifar da irin abin da ya faru a cikin majalisar Jihar kaduna?
” Majalisa da an Sani wuri ne mai tsari domin a nan ne ake yin dokoki na jiha da za su shafi al’umma baki daya domin tabbatar da tsaro da ingantaccen zaman lafiya, saboda haka ta yaya wani ya shiga majalisa wurin yin dokoki a Jihar Kaduna”.
” Ni a iya Sani na a matsayin tsohon dan majalisa, ko shugaban kasa ne zai shiga majalisa sai an gabatar da kudirin shugaban kasa zai shiga kuma an yi tsari kamar yadda majalisar ta tanada, to, ina ga wanda yake haka kawai saket, ba dan majalisa ba ya shiga cikin majalisa har ya tayar da tashin tashina?
Mamadi ya ci gaba da cewa  hakika ya dace a tabbatar an bincika lamarin.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.