Related Articles
Sakamakon Matsalar kamuwar da mutane ke yi da cutar Covid- 19 da ake kira Korona yasa Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin rufe fadar mai martaba Sarkin Daura.
Aminu Masari ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewa an dauki samfurin Jinin mutane sama da Tamanin da aka ta fi da shi Abuja domin yin Gwaji.
Masari ya kuma ce an dauki samfurin jinin me daga mutanen da suke fadar da zagayen fadar domin a tantance lafiyarsu, wanda idan an same su da cutar za a dauki matakin kulawa da su.
Kuma an bayyana cewa an killace dimbin wadansu mutane saboda matsalar cutar Korona.