Home / Labarai / Da dum – dumi: GOBARA TA TASHI A GIDAN SHEIKH GUMI A KADUNA

Da dum – dumi: GOBARA TA TASHI A GIDAN SHEIKH GUMI A KADUNA

IMRANA ABDULLAHI
 GOBARA ta tashi a wani bangare na gidan sanannen Malamin addinin Islama, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi, a cikin garin Kaduna.
Ya zuwa yanzu dai bayanan da muke samu na musabbabin tashin Gobarar ba wasu masu karfi bane, bayannan da muke samu a halin yanzu daga wani da ya nemi a boye sunansa na cewa Gobarar ta tashi ne daga bangaren makarantar Islamiyya da ke gidan.
“Kawai mun dai ga hayaki ne ya na fitowa daga daya daga gillasan makarantar Nan da nan kawai muka jawo hankalin mutane da ke wurin sai kawai muka fara nemo ruwa domin kashe wutar domin kada ta kama dayan bangaren”, inji majiyar.
Zamu kawo maku karin bayanin da ya samu nan gaba

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.