Home / Labarai / Da Dumi dumi: Yan Bindiga Sun Halaka Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina

Da Dumi dumi: Yan Bindiga Sun Halaka Kwamishinan Kimiyya Da Fasaha Na Jihar Katsina

Mustapha Imrana Abdullahi

Rahotannin da muke samu daga Jihar Katsina na cewa an halaka kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta Jihar Katsina Dokta Rabe Nasir.

An dai kashe kwamishinan ne a cikin gidansa da ke rukunin gidaje na Fatima Shema a cikin garin Katsina.

Wata majiya daga bangaren iyalan marigayin na cewa jami’an tsaro sun zagaye gidan marigayin.

ya zuwa rubuta wannan labarin majiyar mu ta tabbatar mana cewa Gawar mamacin na cikin gidan nasa”.

Dokar Rabe Nasir, dai ya samu halartar makarantar jami’ar Abuja,Jami’ar Kansas Lawrence, Jami’ar Bayero Kano, da kuma makarantar Sakandare ta Giwa cikin Jihar Kaduna.

Ya kuma yi aiki da jami’an tsaron yan sandan farin kaya na DSS da kuma hukumar yakida masu kokarin surkusar da tattalin arzikin kasa da kuma harkokin kudi ta EFCC.

Kuma ya ta ba zama dan majalisar tarayya daga shekarar 2007 zuwa 2011, inda ya wakilci kananan hukumomin Mani da Bindawa a majalisar kasa.

About andiya

Check Also

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Jihar Zamfara

APC SAK MATAWALLE GA ZAƁINMU SARKIN SHANUN SHINKAFI MUKE SO Daga Honarabul Abubakar Lauwali kaura …

Leave a Reply

Your email address will not be published.