Home / Labarai / Gwamna Tambuwal Ya Dakatar Da Harkokin Gwamnati, Ya Ziyarci Wuraren Da Yan Bindiga Suka Kai Hari

Gwamna Tambuwal Ya Dakatar Da Harkokin Gwamnati, Ya Ziyarci Wuraren Da Yan Bindiga Suka Kai Hari

 

… Ya Jajantawa Wadanda Aka Kai Wa Harin

 

– Ya bayyana irin taimakon motoci dari biyar “500” da ya ba hukumomin tsaro.

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

 

Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ranar Alhamis ya ziyarci garin Sabon Birni domin yin ta’aziyya iyalan wadanda suka rasa rayukansu mutane 23 a cikin motar Bus da ke dauke da mutane 32 a ranar Litinin.

 

Kamar yadda mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Honarabul Mannir Muhammad Dan’iya shugaban majalisar dokokin Jihar Honarabul Aminu Muhammad Achida shugabannin hukumomin tsaro, kwamishinoni, Gwamnan ya ce “mun zo ne domin mu jajanta maku sakamakon rashin da aka yi”.

Bayanin hakan ya fito ne daga Muhammad Bello mai bayar da shawara na musamman ga Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a kan lamarin kafafe yada labarai da wayar da kan jama’a.

 

 

“Muna addu’ar Allah ya gafarta wa wadanda suka rasa rayukansu ya ba su gidan Aljannah ya kuma ba wadanda suke kwance a asibiti lafiya”.

 

 

Gwamnan ya yi addu’a ya kuma roki Allah ya ba wadanda suka samu kansu a cikin wannan lamari ikon samun saukin abin da suka gani da idanunsu da ya Sanya su a cikin wani yanayi sakamakon harin sauki cikin Sauri

Ya kuma jaddada cewa “Hakika lamarin wani abu ne mai Sosa zuciya irin yadda lamarin ke faruwa a nan da kuma kasa baki daya. A matsayin mu na wadanda Allah ya ba shugabanci a wannan Jihar, hakika mun da mu kwarai da irin yadda wannan lamarin ya faru domin ya ta ba mana zuciya”.

 

“Ba za mu ta ba yin kasa a Gwiwa ba kamar yadda muka yi rantsuwa cewa za mu yi iyakar iyakar mu domin ganin bayan wannan matsalar”.
“Mu na iyakar kokarin mu wajen taimakawa jami’an tsaro a Jihar nan. Mun taimakawa hukumomin tsaro da motoci sama da dari biyar, mun kuma bayar da horo ga jarumai da Gora da ke aikin sa kai sama da dubu daya wadanda aka tantance aka amince da su”, inji Gwamnan.

Gwamnan ya kuma kara da cewa sun kuma bayar da tallafin Baburan hawa ga masu ayyukan da kai domin su samu saukin gudanar da ayyukansu karkashin sa idanun jami’an tsaro

Domin sama wa wadanda lamarin ya rutsa da su sauki Gwamna Tambuwal ya bayyana samar da tallafin naira dubu dari biyu da Hamsin na kashin kansa ga dukkan wadanda lamarin ya shafa, ya kuma bayyana cewa Gwamnatin Jihar za ta biya kudin dawainiyar asibitin dukkan wadanda ke a asibiti su na neman lafiya.

 

Ya ci gaba da cewa za su ci gaba da karfafa ayyukan jarumai da Gora da suke aikin sa kai amma wadanda aka tantance aka amince da su, sabanin irin yadda wadansu kalamai da aka danganta su da dan majalisar Dattawa mai ci yanzu a Jihar cewa an hana ayyukan masu sa kai wato jami’an Bijilante.

“Tambuwal ya kuma yi kira ga daukacin jama’a da kada su Sanya siyasa a cikin lamarin tsaro, inda ya bayyana cewa a cikin wannan watan na Disamba za a ci gaba da biyan jami’an sa kan kudin tallafi na naira dubu Ashirin ta yadda za su samu sukunin gudanar da aikin na su, saboda haka muna kira ga kowa ya bayar da gudunmawarsa wajen ganin an shawo kan wannan matsalar.
Da yake jawabin maraba da Gwamna da tawagarsa shugaban karamar hukumar Sabon Birni Honarabul Umaru Danyaro, cewa ya yi “muna godiya da wannan ziyarar jaje karo a Tara da aka kawo mana domin jajen ta’aziyya zuwa wannan wurin sakamakon aikin yan bindiga da satar mutane a shekara daya da ta gabata.

“Jami’an tsaron da ke nan su na bayar da hadin kai da goyon baya ga karamar hukuma. Don haka abin da ya shafi lamarin tsaro damuwar ba ta Gwamnatin Jiha ba ce ta Gwamnatin tarayya ce.

 

Gwamna Tambuwal na iyakar kokarinsa. Saboda haka mutane su daina yin korafi na suka ga Gwamnati mai ci a yanzu da cewa kamar ta gaza madadin hakan kowa ya duba yadda zai nemi gafarar Allah game da zunubansa na dai- daiku da kuma na jama’a baki day”, shigaban ya jawo hankalin jama’a.

About andiya

Check Also

Muna Kokarin Kafa Hukumar Da Za Ta Hada Hukumomi Wuri Daya Ne – Honarabul Gumi

Bashir Bello majalisa Abuja Honarabul Suleiman Abubakar Gumi wakilin kananan hukumomin Gumi da Bukkum a …

Leave a Reply

Your email address will not be published.