Bashir Bello Majalisar Abuja
Dan majalisar wakilan Najeriya Honarabul Ibrahim Mustapha Aliyu, shugaban kwamitin alternate education ya bayyana dalilin da ya sa yayan kungiyar Filani ta kasa MACBAN suka kawo ziyara majalisar domin su bayyana korafinsu kan batun hade hukumar kula da ilimin yayan makiyaya da masunta da hukumar ilimin manya wuri daya.
Ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawar da manema labarai suka yi da shi a Abuja.
Dan majalisar ya ce dalilin zuwansu shi ne domin yin korafi a kan ta yaya za a hade wadancan hukumomi wuri guda su zama daya ?
Ta yaya bayan kowace hukuma aikin da aka kafa ta daban ne da wancan kuma dukkansu dokar kasa ce ta kafa su ace za a hade su a wuri daya? hakika su yayan kungiyar MACBAN su zo ne a kan wannan batu na hade hukumomi wuri daya.
“Yan kungiyar MACBAN ta Fulani sun shaidawa majalisar cewa hakika su ba su ga amfanin wannan batun hade hukumomin nan ba domin zai ciyar da kasar ne baya kawai, ya kuma tozartar da kyakkyawar niyyar da ita ce tun farko aka kafa hukumomin biyu domin ta saboda haka ne muka ga ya dace lallai mu kira su kuma shi ne suka zo nan suka yi mana cikakken bayani.
” Saboda haka ne wannan abin da muka tattauna da su za mu dauki komai zuwa ga kwamitin da aka Dorawa alhakin hakan”.
A game da batun da su yayan kungiya ta Filani ta MACBAN ke cewa bai kamata a hade wadannan hukumomi guda biyu ba domin daman abin da suke yi daban daban ne kuwa sai dan majalisar ya kada baki ya ce “ai daman kowace hukuma da ka gani doka ta yi ta yan majalisa suka amince kuma ta je wajen shugaban kasa ya amince ya Sanya mata hannu ta zama doka don haka lamari ne da ba wai hannu daya ba ne, koda a bangaren yan majalisar Zartaswa suka fito da wata doka kaga a majalisa ake kawo shi sai kuma majalisar ta zauna a kan lamarin an tattauna domin majalisar ne ke da ikon yin doka idan an kare an bi duk matakai guda uku sannan a kai wa shugaban kasa ya Sanya mashi hannu kuma idan har shi shugaban kasa bai Sanya hannun ba ma sai kawai a dawo da ita majalisa ta dauki mataki a kan kudirin ya zama doka kuma ba a kwance duk wata doka sai an kai gaban majalisar dokoki ta kasa saboda haka su dai sun zo wurin mu”.
“Kuma maganar da suka zo da ita ta na da matukar muhimmanci kwarai domin sun ce dokar da ta kafa wannan hukumar ta makiyaya da masunta ta kasa domin a ilmantar da Mutanensu da ba su zama