Home / Labarai / Dandalin Katsina City News Ya Yantar Da Yan Bursuna, Da Tallafawa Mabukata

Dandalin Katsina City News Ya Yantar Da Yan Bursuna, Da Tallafawa Mabukata

 Imrana Abdullahi
Dandalin Sada zumunta a manhajar Wattsapp da Malam Danjuma Katsina ya kirkiro mai suna Katsina City News ya taimakawa yan gudun hijira da kuma biyawa wadansu mutane kudin tara wanda dalilin hakan suka kubuta saga gidan Yari.
Su dai mambobin wannan dandali sun tara kudi ne ta hanyar yin karo karon a kalla naira dubu biyu ga kowane mutum, wanda sakamakon hakan suka biya wa wadansu yan gidan Yari tara sakamakon hakan kuma suka kubuta daga gidan Yarin
Sun  kuma Tallafawa wadansu mutane da ke gudun hijira daga Batsari, Safana da Kankara da kuma wadansu mabukata a yankin Katsina.
Sun tara kudin ne bayan da suka yi sanarwa a dandalin inda suka ce kowane mamba na wannan dandali ya tallafa da akalla naira dubu biyu kuma an yi katarin samun sa’a daya wa sun bayar da kudin a matsayin Tallafi.
Shi dai wannan dandali ya kunshi mutane da yawa masu bambance bambancen ra’ayin siyasa, Addini da kuma kwararru a fannoni da dama, da suke yin mahawara a kan al’amura daban daban da za su samar da ci gaba a Jihar katsina da kasa baki daya.
A wannan dandali ne aka yi tunanin irin halin da wadansu mutane suke ciki musamman yan gudun hijira da kuma mabuka sai aka yanke shawarar cewa a tara kudi kuma aka Sanya shugabannin da za su kula da abin karkashin Alhaji Lawal Aliyu Daura, tsohon shugaban ma’aikata na Jihar Katsina, da Malam Ibrahim Ahmad Katsina da kuma mutane 21.
Mutane da yawa sun bayar da tallafin kudi da suka hada da mataimakin Gwamnan Jihar Katsina Mannir Yakubu, Alhaji Dahiru Usman Sarki, shugaban gidajen mai na Darma, Alhaji Idris Tune shugaban ma’aikata na Jihar Katsina. Alhaji Lamis Dikko Ajiyan Katsina, Alhaji Mustapha Musa Yar’aduwa, Honarabul Bala Banye, Alhaji Murtala Safana, ofishin PDP Jihar na Katsina, Kungiyar yan jarida reshen Jihar katsina, masu yada labarai a dandalin Sada zumunta da dai sauransu.
Dandalin ya Sanya kwamitoci huda uku, kwamiti a karkashin Barista Ahmad Danbaba da ka Dora masa aikin biya wa yan gidan Yari kudin tara ya kuma samar masu da yanci, sai kuma wani kwamitin karkashin Hajiya Murja Saulawa da aka Dora masa aikin ya sayo kayan da za a Tallafawa jama’a sao kuma kwamiti na uku karkashin Dakta Habib na babban asibitin Gwamnatin tarayya da ke Katsina da zai yi aikin yadda za a yi rabon kayan. Dukkan kwamitocin sun yi aiki cikin nasarar da ake bukatar samu.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun Malam Danjuma Katsian wanda shi me ya kirkiro da wannan dandalin, da fatan Allah ya yi masa sakayya da alkairi.
Masu gudun hijira daga Safana, Batsari da Kankara sun amfana da tallafin kayayyakin rage masu radadi kuma wadansu mabukata da suke kusa da Katsina suma sun amfana.
 Wannan karo na biyar kenan dandalin Katsina city na yin irin wadannan abubuwa na jin kai ga mabukata banda irin taron addu’o’in da dandalin ya shirya saboda ayyukan yan bindiga da ke kai hare hare ann kuma bayar da shawarwari ha Gwamnatin Jihar katsina.
An dai kirkiri wannan dandali ne a shekarar 2015 kuma shi ne kadai dandalin da ke gudanar da aikin sa ba tare da yin harkar siyasa ko nuna bambanci da makamancin hakan. Dandalin ya mayar da hankali ne wajen hada kan  jama’a a karkashin dandalin Sada zumuntar da nufin samar da ci gaba tare da girmama juna ko  a siyasance da tunanin Juna duk kowa na girmama kowa.

About andiya

Check Also

Allah Ya Yi Wa Kanin Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Lawal Isma’il Rasuwa

  Daga Imrana Abdullahi Bayanin da muke samu daga Jihar Kaduna na bayanin cewa Allah …

Leave a Reply

Your email address will not be published.