Home / Big News / Kotun Ta Fi Da Gidanka Ta Ci Shaikh Yusuf Sambo Tarar Naira Dubu 10 A Kaduna

Kotun Ta Fi Da Gidanka Ta Ci Shaikh Yusuf Sambo Tarar Naira Dubu 10 A Kaduna

Imrana Abdullahi
Shahararren Malamin addinin Musulunci shaikh Muhammad Yusuf Sambo Rigachikun ya tabbatar wa manema labarai cewa wata kotun ta fi da gidanka ta ci tararsa tare da Dansa naira dubu 10 a kaduna.
Shaikh Yusuf Sambo ya bayyana cewa ya samu gayyata ne daga gidan Rediyon Jihar Kaduna ( KSMC) domin amsa wadansu tambayoyi domin amfanin al’umma baki daya.
” Na fita daga cikin gidana tun misalin karfe Bakwai da wani ABU domin cika lokacin da aka ce na gidan Talbijin na KSMC karfe Takwas za a gudanar da shirin don haka na Isa kafin karfe 8 na safe, bayan mun kammala shirin sai na cewa Dana da na ta fi da shi wato Suhaibu, cewa mu ta fi yi wa wani aminina Alhaji Ado Fara, ta a ziyyar mahaifiyarsa, bayan mun gama sai na ce mu bi ta titin Jami’ar Jihar Kaduna KASSU, muna isa dai dai mararrabar wurin sai Naga wasu yan sanda ina tsayawa sai kawai wani ya ce mini kuje can ana nemanku, da isar my Naga wata alkaliya zaune a wurin wato Majistare ana ce mata Sa’adatu, kuma ga masu karbar kudi Tasks force”.
” Nan take aka ce gani ansa dokar batun Takunkumi kuma wanda ba shi da shi sai ya biya naira dubu biyar, ina tare da Dana ne shima aka ce masa naira dubu biyar kudi suka kama dubu Goma, ba a tambaye ni ba asin komai ba sai dai kawai in bada kudi nan take na ciro na biya na ce a bani rasidi nawa daban na Dana daban”. Inji Malam.
Malamin ya kara da cewa shi a iya saninsa ba haka ake yin lamarin kafa kotun shari’a ba sai a kaiwa majalisar dokoki ta Jiha su tabbatar da doka kuma a gayyaci jama’a ayi taron sauraren jin ra’ayin jama’a duk a kaduna ba a yi hakan ba, sai kotun kawai ana yi wa jama’a tara duk da ga halin da ake ciki to, ina ga wanda bashi da kudin da zai biya yana ta kansa ya samu abin da zai ci a ina zai Nemo irin wadannan kadade?
Shaikh Sambo Rigachikun ya ci gaba da cewa ko kowa bai san tasirin yin addu’a ba mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya Sani domin lokacin da yake waje yana neman lafiya sai da kowane bangare na mutanen kasar nan ya dage yi masa addu’a Musulmi da Kirista kuma Allah ya karbi addu’ar an samu lafiyar tare da nasara.
“Ai idan lokacin zabe ya zo Malamai ake nema haka nan idan akwai wata musiba a kasa duk malamai ake nema domin su yi addu’a Allah ya kawo sauki a kasa, Kuma game da wannan ciwo na Korona bairus an ce an tambayi Ahaluzzikiri, wato ma abota Sani to yasa a bangaren addini ba a tambayi Malamai ba domin a samu warware matsalar cikin ruwan sanyi”.
Kuma ma abota ilimi da malamai duk sun san matsayin Masallaci da kuma kasuwa, amma an rufe masallatai an bude wasu kasuwanni na daban, to me yasa?
Masallatai fa dakin Allah ne wurin yin addu’o’i, kasuwa kuma addini ya tabbatar mana cewa matattara ta wadansu irin mutane yana nan a cikin karantarwar musulunci.

About andiya

Check Also

KATSINA IZALA GROUP CONSTRUCTS EYE HOSPITAL

  Work has been progressing steadily at the site for the construction of Eye Specialist …

Leave a Reply

Your email address will not be published.