Home / KUNGIYOYI / DANGOTE YA SAMAR DA MASU MILIYOYI NAIRA  A KANO
Daga hagu zuwa Dama Daraktan sayar da kaya ne na kamfanin na yankin Arewa maso Yamma Aliyu Dan Aliyu, sai wanda ya lashe Gasar Miftau Shu'aibu Aliyu da kuma shugaban Sayarwa da tallace tallace na kamfanin Sumuntin Dangote Rabi'u Umar Umar wajen mikawa kyaututtuka a 

DANGOTE YA SAMAR DA MASU MILIYOYI NAIRA  A KANO

Daga Imrana Abdullahi
A kokarin kamfanin Dangote na ganin an Tallafawa al’umma domin kowa ya dogara da kansa kamfanin Sumunti na Dangote ya bayar da miliyoyin naira ta mutane biyar.
Da yake jawabi a wajen bayar da Cekin kudi ga mutane biyar da suka samu nasarar lashe gasar, babban jami’in da ke kula da sashen ciniki da tallace- Tallace, Rabi’u Umar cewa ya yi wannan gasar da kamafanin ke gudanarwa ana tsari ne na yi wa al’umma hidima daga cikin irin abin da kamfanin ya samu musamman a tsarin taimakawa masu hulda da kamfanin.

Daga hagu zuwa Dama Daraktan sayar da kaya ne na kamfanin na yankin Arewa maso Yamma Aliyu Dan Aliyu, sai wanda ya lashe Gasar Miftau Shu’aibu Aliyu da kuma shugaban Sayarwa da tallace tallace na kamfanin Sumuntin Dangote Rabi’u Umar Umar wajen mikawa kyaututtuka a
Ya ce wannan tsarin gasar da ake yi kashi na uku an tsara ne kamfanin ya ba masu hulda da shi makudan kudi a kalla naira biliyan daya ga kwastomomin kamfanin da ke fadin Najeriya baki daya, wanda hakan zai ba su damar samun ingantawar tattalin arziki da zuba jari  a kasa baki daya.
Babban jami’in sayar da Sumuntin Dangote Aliyu Dan Aliyu shawara ya ba wadanda suka samu nasar ya yi hakika ya dace su isar da wannan sakon ga dimbin mutanen da suke nesa da wannan wuri da nufin suma su amfana da tsarin idan an sanar da su.
 “Masu saye da raba wannan kayan, da kuma sauran yan Najeriya, za su iya zama sun mallaki miliyoyin kudi, sakamakon wannan shirin da shugaban kamfani Aliko Dangote ya samar duk an yi hakan ne da niyyar kara inganta rayuwar yan Najeriya,musamman a wannan yanayin da ake ciki na batun kalubalen tattalin arzikin da kasa ke fuskanta”.
Kamfanin Sumuntin na Afrika, a watan Yuli suka fitar da Dangote ya zama miloniya a karo na uku a fannin gasar kamfanin Sumuntin Dangote ta kasa, a Legas a lokacin ne kamfanin ya bayyana cewa masu hulda da kayan kamfanin mutane 500 za su samu naira miliyan daya kowannensu sai kuma wasu mutane 100 da za su samu miliyan biyar  a cikin watanni hudu.
Wadanda suka samu nasarar lashe gasar sun hada da: Messr Auwal Abdullahi, Isyaku Yinusa, Idris Ibrahim Haruna, Miftau Shu’aibu Aliyu da Jamilu Rshaif Idris.
Da yake zantawa da manema labarai, wani da ya samu nasara, Auwal Abdullahi, mai shekaru 31, kuma mai yaya uku ya jinjinawa kamfanin Dangote kwarai inda ya ce mai yuwuwa shi ne miloniya na farko a cikin dangansa.
Ya yi alkawarin cewa zai yi amfani da kudin kamar yadda ya dace ta hanyar zuba jarinsa wajen sana’ar Sumuntin, da kuma wajen taimakawa iyalansa a game da bukatunsu.
Gasar kashi na uku ana saran za ta samar da mutane 125 da suka samu miliyoyin naira a wata wata daga cikin biliyan daya da za su lashe kudi da kuma makamancin hakan.

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.