Home / Kasuwanci / ZA A GINA SABUWAR KASUWA A GEIDAM

ZA A GINA SABUWAR KASUWA A GEIDAM

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe ya rattaba hannu kan kwangilar N3.8bn ga gina sabuwar kasuwa irin ta zamani  a garin  Geidam kamar yadda gwamnatin sa ta yi alkawarin yi.

Gwamnatin Yobe da kamfanin gine-gine na Green and Blue Communications & Electronics Ltd., suka rattaba hannu kan kwangilar gina kasuwar Geidam ultra-modern kan Naira biliyan 3.8 a garin Damaturu.
Kamar yadda wakilinmu ya ruwaito cewa, Alhaji Barma Shetima, kwamishinan kasuwanci, masana’antu da yawon bude ido na jihar da Malam Kura Goni-Mama ne suka sanya hannu kan kwangilar a madadin jihar da kamfanin.
Da yake jawabi a wajen taron, Shetima ya ce an bi tsarin da duk ya dace wajen bayar da kwangilar da za a kammala cikin watanni 12 kamar yadda aka alkawarta.Ya bayyana cewa, wannan sabuwar kasuwa irin ta zamani da za a gina a garin na Gaidam ta kunshi, magudanar ruwa, masallaci, bandakunan jama’a, shaguna 500, rumfuna, da Hanyoyi da katangar kewaye ta da sauran abubuwan more rayuwa.

Kwamishinan ya bukaci dan kwangilar ya yi aiki mai kyau daidai da yarjejeniyar kwangilar da aka Rantaba Hannu akai.

Shetima ya ce aikin na daga cikin shirin Gwamna Mai Mala Buni na bunkasa harkokin kasuwanci da inganta kudaden shiga da ake samu a cikin gida da samar da ayyukan yi a jihar.Ya ce an kammala irin wannan aikin kasuwa a Gashua kuma za a kaddamar da shi a ranar 3 ga watan Satumba, yayin da wasu uku a Nguru, Potiskum da Damaturu, sun kai matakai daban-daban.

A nasa jawabin, Goni-Mama ya godewa jihar bisa baiwa kamfaninsa kwangilar tare da yin alkawarin gudanar da aiki mai inganci cikin wa’adi da aka alkawarta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa Alhaji Bukar Mustapha, memba mai wakiltar Geidam ta tsakiya a majalisar dokokin jihar ne ya shaida taron;  da Alhaji Bukar Dauda kwamishinan gidaje da raya birane.

In ba a manta ba an dade ana takaddama da kungiyar ‘yan kasuwar garin na Gaidam dangane wurin da ya dace don gina kasuwar yadda wasu daga cikin su ke cewa ba su amince da tada su a Kasuwar da su ke a yanzu ba mai dauke da dubban shaguna da zimmar za a gina musu wata kasuwar da ba za ta  iya daukar ko da rabin’ yan kasuwar ba kamar yadda shugaban kungiyar Alhaji Abba Gaidam cikin wata tattaunawa da suka yi da Wakilin namu a baya can.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.