Home / News / Dattawan PDP Zamfara sun roki Ayu da ya sanya baki akan matsalar su da dan takarar Gwamna

Dattawan PDP Zamfara sun roki Ayu da ya sanya baki akan matsalar su da dan takarar Gwamna

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Gamayyar kungiyar Dattawan jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara sun yi kira ga shugaban jam’iyyar na kasa Dokta Iyorchia Ayu da ya Sanya baki domin ceton jam’iyyar daga cikin halin da ta shiga.
Sun dai bayyana hakan ne a cikin wata takardar da suka raba wa manema labarai mai dauke da sa hannun Alhaji Musa Umar Dangulbi, Shugaban gamayyar kwamitin Dattawa masu taimakawa jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa Biyo bayan rushe zaben Gwamna na fitar da Gwani na jam’iyyar PDP reshen Jihar Zamfara,gamayyar kungiyoyin Dattawa masu taimakawa PDP sun wanke bangaren shari’a daga dukkan zargi game da hukuncin da kotu ta yanke.
Gamayyar kungiyar, ta bayyana hukuncin da  Alkali Aminu Bappa a ge da lamarin PDP da ya yanke cewa jam’iyyar ba za ta tsayar da dan takarar Gwamna ba a lokacin zaben shekarar 2023 mai zuwa a matsayin wata magana ce da ta faru sakamakon irin rashin jituwa da kuma jiji- da – kai a tsakanin yayan jam’iyyar musamman rashin tabbatar da raba dai dai, hadin kai da kuma yi wa kowa adalci ga tsofaffin magoya bayan PDP a Jihar Zamfara daga dan takarar Gwamnan Jihar Dauda Lawal Dare da kuma wasu shugabannin jam’iyyar na kasa a Abuja.
Kuma mun Dora laifi ne ga wasu mutane yan kalilan a cikin jam’iyyar a babban ofishin PDP da ke Abuja da suke yin aiki tare da Dauda Lawal,da sula rika kawowa duk wani kokarin samun dai- daito da maslaha a tsakanin yayan jam’iyyar a matakin Jiha.
Hakika wannan kalubalen da bashi da dadin ji da ya samu jam’iyyar PDP da dan takarar Gwamna da ya haifar da soke zaben fitar da dan takarar Gwamna na farko da na biyu, da muka rubuta wa uwar jam’iyyar domin dawo da hankalinta bukatar da ake da ita a samu dai- daitawa a tsakanin yayan jam’iyyar a game da batun zaben shugabannin jam’iyya.
Gamayyar kungiyoyin, sun ce amma sakamakon irin yadda aka hada kai da wasu mutane daga Abuja aka yi Sauri wajen sake zaben fitar da dan takarar Gwamna, ba tare da sanin sauran yan takarar Gwamna ba.
“A matsayin mu na masu ruwa da tsaki , zan iya tabbatar maku cewa, masu yin zaben dan takara daga kananan hukumomin Gumi,Zurmi, Talatar Mafara, Bukkuyum da karamar hukumar Anka duk ba su ma san inda aka gudanar da zaben fitar da dan takarar ba amma kuma aka bayyana sakamakon zabe.
“Shi kuma dan takarar Gwamna Dauda Lawal, sai kawai ya watsar da jam’iyyar a matsayinsa na dan takarar Gwamna ya koma kasar Dubai kawai.Muhimmin mutum kuma jagoran jam’iyyar kamar Aliyu Gusau, da sauran su da yawa duk an yi watsi da su a wajen gudanar da al’amuran jam’iyyar tun lokacin da Dauda Lawal ya zama dan takarar jam’iyyar.
“Wani abin bakin ciki ma da ya faru shi ne a lokacin da shugaban jam’iyyar na Jihar Zamfara ya rasu ba dan takarar Gwamna da ya dace Dauda Lawal ya jagorance mu a wajen makoki duk ko a wannan yanayin ma duk ya yi watsi da mu kawai.
” Saboda haka muna yin kira ga shugaban jam’iyyar mu na kasa da ya samu wani lokaci na musamman domin muna sane da irin yadda ayyuka suka yi masa yawa, ya warware matsalolin da tun a can baya muka gaya masa domin dawo wa da martabar jam’iyyar”.

About andiya

Check Also

An Rantsar Da Ishaya Idi Sabon Shugaban Kasuwar Duniya Ta Kaduna

  Daga Imrana Abdullahi A kokarin ganin al’amura sun ci gaba da tafiya kamar yadda …

Leave a Reply

Your email address will not be published.