Home / KUNGIYOYI / Kungiyar Mawallafa Sun Karrama Yusuf Umar Garkuwa

Kungiyar Mawallafa Sun Karrama Yusuf Umar Garkuwa

Daga Imrana Abdullahi

Sakamakon irin kokarin ganin ya Tallafawa rayuwar marasa karfi da ke cikin al’umma ta fuskar ilimi, koyar da sana’o’i, kula da lafiya da sauran hanyoyin inganta rayuwar al’umma hakan ta Sanya kungiyar masu wallafa jaridu da mujallu na arewacin Najeriya karkashin “Arewa Publishers Forum”, suka Karrama Yusuf Umar Garkuwa da lambar karramawa da nufin ya ci gaba da samun kwarin Gwiwar aiwatar da wadannan ayyukan ciyar da rayuwar marasa karfi gaba.

A wani kwarya kwaryan taron da ya gudana a garin Kaduna  ne aka yi taron karramawar.

Jim kadan bayan karbar lambar yabon Yusuf Umar Garkuwa ya bayyana matukar jin dadinsa da wannan karramawa.

Yusuf Garkuwa ya ce an shaida masa cewa za a bashi wannan lambar karramawa ne don haka bai yi tsammanin cewa irin abubuwan da yake yi ba akwai wadanda suke ganin abubuwan kuma har suka ga dacewar ayi hakan, amma dai hakika muna yi wa Allah godiya a kan hakan.

“Koda siyasa ko ba siyasa hakika zamu ci gaba da ayyukan taimakawa jama’a da nufin inganta rayuwar jama’a a cikin al’umma”.

Hakika na ji dadi kuma abin ya ba ni mamaki kwarai matuka da wannan karramawar da aka bani.

“Sai da na lura cewa duk abin da mutum yake yi na kyautatawa al’umma komai kankantarsa akwai wadanda suke kallon hakan. Abubuwan da muke yi a bangarorin da suka hada da ilimi da kuma sana’o’i koda siyasa ko ba siyasa zamu ci gaba da yin hakan domin ba muna yin saboda siyasa ba ne kawai, kasancewar Gwamnati kadai ba za ta iya wadatar da al’umma ba dole ne sai masu zaman kansu sun shiga cikin lamarin don haka ne muke shiga wajen harkar inganta rayuwar jama’a a Tallafawa gwamnati a samu biyan bukata.

Kuma “nima daga yanzu duk abin da ya shafi kungiyar Arewa publishers Forum, ya share ni, za a ci gaba da yin hulda sosai don haka na zama dan kungiya ta bangaren abokantaka ko zumunci, don haka ina godiya kwarai”.

Tun da farko a cikin jawabinsa a madadin yayan kungiyar Dokta Sani Garba cewa ya yi wannan kungiya ta mawallafa jaridu da mujallu suna kokarin bincike ne domin lalubo wadanda suke bayar da gudunmawar ci gaban al’umma wanda hakan na taimakawa kokarin da Gwamnati ke yi a kowane irin mataki na rayuwar jama’a.

Mun duba irin yadda Yusuf Umar Garkuwa ke kokarin daukar nauyin koyawa jama’a sana’o’i da kuma harkokin ilimin jama’a da sauran wadansu fannonin kyautata rayuwa baki daya, don haka muka ga cancantar wanda hakan zai kara masa kwarin Gwiwa har wasu kuma su yi koyi da abin da yake yi.

About andiya

Check Also

Samar Da Tsaro Sai Kowa Ya Bayar Da Gudunmawarsa – Kaftin Joji

….A koma ga masu unguwanni, dagatai da hakimai Kaftin Muhammad Joji ya bayyana cewa lallai …

Leave a Reply

Your email address will not be published.