Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Wani fitacce daga cikin masu zaben Sarki a masarautar Zazzau, Limamin Konan Zazzau Malam Sani Aliyu ya rasu.
A cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun masarautar Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta bayyana rasuwar Limamin a daren yau Alhamis.
“Allah ya yi wa Limamin Konan Zazzau rasuwa Malam Sani Aliyu, daya daga cikin mutane biyar masu zaben Sarki a masarautar Zazzau wanda shi ne babban Limamin masarautar”, inji sanarwar.
Sanarwar ta bayyana cewa za a yi Jana’izarsa da karfe Sha daya na safiyar Gobe Juma’a 30 ga watan Yuli, 2021.