Home / KUNGIYOYI / Jihar Zamfara Za Ta Ziyarci Mutanen Ta A Kudancin Najeriya

Jihar Zamfara Za Ta Ziyarci Mutanen Ta A Kudancin Najeriya

 

Imrana Abdullahi Daga Kaduna

 

A kokarin Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawalle na ganin ya kare martaba da mutuncin al’ummar Jihar Zamfara ya bayar da umarni ga mai bashi shawara a kan harkokin hulda da kasashen waje da kungiyoyi Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya kai ziyara ga yan asalin Jihar Zamfara da ke zaune a wasu Jihohin kasar.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya bayyana wa wakilin mu cewa tuni Gwamna Muhammadu Bello Matawalle ya amince da a kai wa yan asalin Jihar da ke zaune a Jihohin Legas, Edo, Ondo, Kwara, Abuja da kuma Kaduna ziyara domin ganin irin halin da suke ciki da kuma fadakar da su game da wasu muhimman al’amura.

“Za mu kai ziyara zuwa wadansu Jihohin da muka lissafa domin fadakar da yan asalin Jihar Zamfara muhimmancin dawowa gida domin yin zabe idan lokaci ya yi sai kuma muhimmancin zama lafiya da Kaunar Juna”.

Ya ci gaba da bayanin cewa tare da tawagarsa zai kai ziyara Jihar Edo domin a tattauna da mahukuntan Jihar game da irin yadda yana salin Jihar Zamfara ke ciki a lamarin zamantakewar su da hullodinsu na yau da kullum.

Kamar dai yadda Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya sanar cewa ana saran tawagar ta sa ta kwashe kwanaki uku a yankin Kudancin Najeriya a lokacin ziyarar.

“Tuni dai har mun sanar da daukacin shugabannin yan asalin Jihar Zamfara da ke zaune a wadannan Jihohin da za mu ziyarta domin su shirya karbar bakuncin tawagar mai bayar da shawara ga Gwamnan Jihar Zamfara a kan hulda da kasashen waje da kungiyoyi da nufin samun nasarar kwalliya ta biya kudin sabulu.

 

Akwai muhimmanci kwarai ga yan asalin Jihar Zamfara kowa ya dawo gida lokacin zabe domin kada kuri’arsa, sai kuma muhimmancin zaman lafiya da mayar da hankali a kan neman halak.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.