Home / Labarai / Duk Masu Son Shiga Tsakaninmu Da Hukuma Ba Za Su Samu Nasara Ba – Shaikh Gumi

Duk Masu Son Shiga Tsakaninmu Da Hukuma Ba Za Su Samu Nasara Ba – Shaikh Gumi

Mustapha Imrana Abdullahi
Sakamakon irin rade- radi da jita jitar da ake ta yadawa cewa wai jami’an tsaron Yan Sandan farin kaya sun kama Shaikh Dokta Ahmad Muhammad Abubakar Gumi, ya sa Malamin da kansa ya fito fili ya yi bayanin cewa masu son raba tsakaninsa da hukuma ba za su ci nasara ba.
Shaikh Dokta Ahmad Gumi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wa’azin da ya saba gabatarwa na littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.
“Hakika irin wannan al’amarin za a iya cewa wadansu ne masu kokarin sai dole sun raba tsakanina da hukumomin jami’an tsaro kuma da ikon Allah ba za su samu nasarar yin hakan ba.
“Muna shiga cikin daji ne domin jawo hankalin mutanen da suka koma dajin su Sani cewa abin da suke aikatawa ba dai dai ba ne domin laifi ne har a wurin Allah, kuma su Sani cewa su ma mutane ne kamar kowa masu yanci kamar yadda muma muke da yanci da hakki a wurinsu don haka su rungumi hanyar Allah a samu zaman lafiya da ci gaban da kowa ke bukata”.
Ya ci gaba da bayanin cewa ” mutanen nan su na ganin mu cewa mu malamai ne da ke yin wa’azi don haka ne ma suka saurare mu har muka je wurinsu muka yi masu wa’azi tare da muhimman jawabai da jan hankali game da abin da Allah ya fadi kan samun zaman lafiya”.
Saboda haka mu a koda yaushe manufarmu its ce a samu zaman lafiya da ci gaban kasa, masu kokarin ganin an samu wani abu da ba haka ba su na batawa kansu lokaci ne, domin muna yi don Allah ne ba domin duniya ba”.
“Muna sane da cewa dukkan abin da ya baci malamai ne za su iya kawo gyara ba yan siyasa ba ko masu kama da haka, saboda malamai na kokarin dabbaka kalmar Allah ne domin kowa ya ji ya kuma bi abin da Allah ya fadi”.
Mutane su rabu da masu kokarin yada jita jita su ji dan sanyi a zuciyarsu sakamakon abin da ke idanunsu a zuciyar.

About andiya

Check Also

Shekara Ɗaya A Ofis: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Muhimman Ayyuka A Wasu Ƙananan Hukumomin Zamfara

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka a Ƙananan Hukumomin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.