Home / Labarai / Duk Masu Zaton Buhari Ne Zai Magance Matsalar Tsaro Sun Yi Kuskure

Duk Masu Zaton Buhari Ne Zai Magance Matsalar Tsaro Sun Yi Kuskure

Duk Masu Zaton Buhari Ne Zai Magance Matsalar Tsaro Sun Yi Kuskure
Mustapha Imrana Abdullahi
Wani Jigo a Jam’iyyar APC Alhaji Musa Abubakar Dan Malikin Arugungu, ya gargadi al’umma da su koma ga Allah domin samun warware matsalar tsaron da Nijeriya ke fama da ita.
Alhaji Musa Abubakar ya bayyana cewa ta yaya duk wadanda aka ba amanar kawo kariya ga kasa sai a rika ganin abubuwa na tafiya ba dai- dai ba.
Ya bayar da misali da cewa irin yadda a kwanan baya aka samu wani mai shigowa da miyagun makamai ta kan iyakar Nijeriya abin mamaki ne ” wanda aka samu da miyagun makamai har da makami mai harbo Jirgin sama, da aka samu mutumin a Katsina, shin ina masu aiki a bakin kan iyakoki har wannan mutum ya shigo da wadannan miyagun makamai?
Alhaji Musa Abubakar Dan malikin Arugungu wanda ya kasance dan siyasa,dan kasuwa kuma Manomi ya ankarar da jama’a cewa kowa zai ya bayar da ta sa gudunmawar domin gyaran kasa, amma ba a zurawa Buhari idanu shi kadai ba.
” sai kaga jami’an tabbatar da tsaro sun shigo cikin gari kan tituna amma ga kan iyakoki an bar su an shigo gari ana tsare ababen hawa ba gaira ba dalili”.
Mutanen Nijeriya su guji aikata cin hanci da karbar rashawa domin kasa ta zauna lafiya.
Ya kuma yi kira ga shugabanni da su hanzarta daukar matakan yin addu’a ta hanyar Sanya wadanda suka san yadda ake rokon Allah a gaba ta fatan samun hanyar warware matsalar da ke addabar Nijeriya.
“Shugaba Buhari ba shi ne zai warware matsalar kasar nan shi kadai ba kowa na da irin gudunmawar da zai iya bayarwa a samu nasarar da ake bukata.
Dan Malikin Arugungu ya ci gaba da yin kira ga mutanen karkara da su rika bin dokar kariya ga cutar Korona, kasancewa cutar gaskiya ce ba kamar yadda ake samun sakaci a yankunan karkara
“Matsalar shaye shaye ta dade a cikin al’ummar Nijeriya don haka jama’a su fahimci irin yadda ake samun illar shan miyagun kwayoyi, don haka muna kira ga daukacin jama’ar Nijeriya su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga sabon shugaban hukumar yaki da hana sha da miyagun kwayoyi Janar Buba Marwa domin ya samu nasarar da za ta amfani kowa”.
Ya yi kira ga hukumomi da su guji sakin wadanda aka samu da matsalar kwayoyi, musamman ga masu bayar da matsugunni ga masu sayar da kwayoyi ko kayan maye a cikin al’umma.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.