Home / Big News / Buhari Ya Nada Zanna Mohammaed Ibrahim Shugaban Yan Sanda

Buhari Ya Nada Zanna Mohammaed Ibrahim Shugaban Yan Sanda

Buhari Ya Nada Zanna Mohammaed Ibrahim Shugaban Yan Sanda

Mustapha Imrana Abdullahi

 

Shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya nada mataimakin shugaban yan sandan kasar Zanna Mohammed Ibrahim, a matsayin shugaban riko na Yan Sanda.

 

Shi dai wanda aka nada a halin yanzu ya zama shugaban riko dan asalin Jihar Borno ne da ya ta ba zama kwamishinan Yan Sandan Jihar Delta da Zamfara kafin ya samu karin girma zuwa matsayin mataimakin shugaban Yan Sanda na kasa.

 

Shi dai Mista Ibrahim an haife shi ne a watan Nuwamba, ranar 26, 1962.

 

Ya samu shaidar karatun Digiri a kan fannin kimiyyar Siyasa da kuma digiri na biyu a kan dangantakar huldar kasa da kasa tare da ayyukan tsare tsare duk a jami’ar Jo’s, da ke Jihar Filato.

 

Ya shiga aikin dan Sanda a ranar 15 ha watan Maris, 1988.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.