Related Articles
MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
GWAMNAN Jihar Zamfara Alhaji Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa daga yau babu sauran wanda zai kara bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a Jihar, in ba wanda uwar jam’iyya ta kasa ta mikawa takardar shahada ba su ne shugabanni.
“Duk wata shedana da kuma yin taron gangamin siyasa ko bude wani ofishin jam’iyya na daban babu shi.”
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yi wa shugabannin jam’iyyar jawabi jim kadan bayan da suka karbi takardar shaidar cewa su ne halartattun shugabannin APC a Jihar Zamfara.
“Batun duk wata shedana ko bude wani ofishi da sunan ofishin jam’iyya duk ya kare a Jihar Zamfara, saboda akwai mai bayar da shawara a kan harkokin gidaje zan bashi umarnin cewa duk wanda ya bude wani ofishi a ko’ina ne da sunan ofishin APC to a dauki mataki a kansa kamar yadda shari’a ta tanadar”.
Gwamnan ya kara da cewa tun da dai ba a busa begilan siyasa ba to, kada kowa ya sake yin wani gangamin siyasa har sai lokacin da aka bayar da damar fara siyasa.
“Hakika duk mun yi hakuri da abin da ya faru can baya, amma a yanzu komai ya zo karshe domin hukumar zabe ta bayar da takardu ga halartattun shugabannin jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, don haka babu sauran wata shedana ko wani ya boye a wani wuri ya Iza ayi ta yin abin da bai dace ba”. Inji Gwamna Matawalle.