Home / Ilimi / Farfesan Ilmin Arabiya Ya Bukaci A Kwace Lasisin Jardar Sahara Reporters

Farfesan Ilmin Arabiya Ya Bukaci A Kwace Lasisin Jardar Sahara Reporters

 

Wani Farfesan ilmin Arabiya, Farfesa Mohammed Shafiu Abdullahi ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta kwace lasisin wallafa jaridar Sahara Reporters bisa kokarin su na raba kan al’uma, haddasa fitina da kuma batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Ya nuna wannan bukata ne sailin da take tofa albarkacin bakin sa bisa labarin batanci da jariadar ta wallafa a makonnin da suka gabata.

Yace duk da jaridar ta cire labarin daga manhajarta tare da bada hakuri, farfesa Shafiu Abdullahi yace “Tubar Muzuru ne”.

Domin kuwa a cewarsa ” Mai hali baya daina halinsa”.

Farfesan Wanda har ila yau shine Jagoran hukumar kula da ilmin Islamiya da karatun Arabiya na kasa dake kaduna, Yayi zargin cewa, kwata kwata jaridar bata son duk wani abinda ya shafi addinin musulunci da musulmi.

Ya tuno yadda jaridar tayi rubutun batanci akan hukumar da yake jagoranta. Inda suka yi zargin cewa gwamnati na ba hukumar biliyoyin nairori don gudanar da manyan ayyuka amma kuma ana rub da ciki da kudaden.

Shugaban hukumar yayi mamakin yadda zaa ba da kudade don ayyuka amma kuma baayi sannan gwamnati bata dauki wani mataki ba. ” Shin ita kan ta Ma’aikatar Ilmi ta tarayya ina ta ga biliyoyin nairori har da zata baiwa wata hukuma.” Farfesan yayi tsokaci.

Yace Sahara Reporters sun zarge shi da daukar ma’aikata yan asalin yankin sa kadai, Wanda yace hakan ba zai taba yiwuwa ba domin kuwa ba kamfani bane na kashin kansa.

Dangane da zargin hukumar da jaridar tayi akan handane kudaden albashi kuwa, Farfesa Shafiu Abdullahi yace wannan ma abin dariya ne da kuma rashin yadda aka gudanar da ayyukan gwamnati.

Ya ce “Babu yadda za’ayi aci kudin albashin ma’aikata domin kuwa dukkan Ma’aikatan gwamnatin tarayya suna cikin tsarin nan da aka sani da suna IPPIS.Wanda ta nan ne daukacin albashin ma’aikatan gwamnatin tarayya da hukumomi ake biyan su kai tsaye ba tare da kudin su ya biyo ta hannun kowa ba daga Abuja.

Masanin ilmin Arabiyan ya ce jaridar Sahara Reporters kafa ce da ta zama ta ‘yan baranda wadanda ke wa makiya musulunci da makiya zaman lafiya suke wa aiki.

Ya shawarci al’ummar najeriya musamman musulmi da su nisanta kan su day wannan jarida tare da nuna masu kiyayya domin dakushe karfin su da gurgunta al’amurran su wajen cigaba da gudanar da ayyukansu na batanci ga al’umma.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.