Home / Big News / Ga Jawabin Gwamnan Kaduna Game Da Cutar Korona birus

Ga Jawabin Gwamnan Kaduna Game Da Cutar Korona birus

Korona Birus: Jawabin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai Game Da Tsauraran Matakan Da Gwamnati Ta Dauka Domin Dakile Yaɗuwar Cutar Korona Baros

Ya ku al’ummar Jihar Kaduna,

Abin takaici ne yadda Cutar Korona Baros ta shigo kasarmu Nijeriya. A yau ina magana da ku ne domin in kara jaddada muku irin hadarin wannan annobar cewa gaskiya ce. Wannan cuta ta Korona Baros ta yi wa kasashe da dama lahani sosai har da kasashen da suka ci gaba. Ba hanyar da za mu yi domin magance wannan annoba sai ta hanyar daukan matakin riga-kafi domin dakile yaduwar wannan cuta.

Lura da irin halin da kasarmu take ciki, babu wani abin da za mu kare a’ummarmu illa mu dauki duk matakan da za mu dauka domin dakile yaɗuwar cutar. Ranar Juma’a ni da mataimakiyata Dakta Hadiza Balarabe mun ɗauki awa biyu mun yi hira kai tsaye da al’umma mun bayyana wa al’umma irin hadarin wannan cuta. Mun bayar da shawarwarin da za a bi domin kare kai da kamuwa da wannan cuta wanda suka haɗa da tsaftan kaya da muhalli da wanke hannu da sabulu da kuma kaurace wa tarurruka. Sannan kuma muka bayar da sanarwar hana tarurruka tare da ba shugabannin addinai shawarar a dakatar da duk wasu tarurruka na jama’a kamar yadda masana kiwon lafiya suka bayar da shawara.

Muna gode wa shugabannin addinan da suka ba mu goyan baya game da barin tarurruka, sannan mun yi takaicin wadanda suka bijirewa wannan shawara. Mun samu rahoton wadanda suka yi tarurruka na ibadu a coci coci da masallatai da kuma sauran tarurruka na bukukuwa.

Wannan ya nuna irin waɗannan mutanen har yanzu ba su san irin hadarin da ke tattare da bala’in da muke fuskanta ba. Duk da cewa har yanzu babu mutum ko ɗaya da ya kamu da wannan cuta ta Korona Baros, ba za mu yi ƙasa a gwiwa ba wurin kare rayukar al’ummarmu. Saboda haka za mu ɗauki duk matakin da ya dace domin hana yaɗuwar wannan cutar.

Saboda haka Gwamnatin Jihar Kaduna ta canza matsaya, daga matsaya ta bayar da shawara zuwa sanya doka na hana duk wasu tarurruka musamman a masallatai da coci coci. An ba jami’an tsaro umurnin su tabbatar an yi aiki da wannan dokar a fadin jihar baki ɗaya. Sannan kuma su tabbatar duk wasu makarantu an kulle su, har da makarantu masu zaman kansu da Islamiyyu da na allo da kuma makarantun mishan na kiristoci.

Gwamnati a shirye take ta sanya dokar-ta-ɓaci ta hana fita in har ita ce kaɗai hanyar da zai sa mutane su bi wannan doka kuma mutane su fahimci irin haɗarin wannan cutar. Riga-Kafi ce kaɗai hanyar da za mu bi domin daƙile yaduwar wannan cutar saboda ba mu da liktoci da magungunan da za mu iya magance wannan cutar in ta bi garuruwanmu da ƙauyukanmu. Gara mu dauki duk matakin da ya kamata na dakile wannan cutar ta Korona Baros da mu zo muna birne mutanen da suka mutu. Muna kallon irin kasashen da suka yi sakaci ko suka ƙi ɗaukan matakai yadda suka zo suna da-na-sani.

Saboda haka, muna ƙara ba jama’a shawara su bar yawace-yawace su zauna a gidajensu har sai ya zama dole. A soke duk wasu tafiye tafiye har sai an ga bayan wannan annobar saboda ai ana raye sannan ake iya tafiye tafiye. Don Allah ku kare rayukanku da na ‘yan uwanku. A bisa wannan dailin ne muka buƙaci a dakatar da jigilar fasinjoji daga Abuja zuwa Kaduna a jirgin ƙasa saboda hana mutanen da watakila sun kamu da cutar su shigo mana jiha.

Muna kira da duk waɗanda suka dawo daga tafiye tafiye daga ƙasashen Turai kwanaki 14 da suka wuce da su killace kansu kuma in suka ji wata alama ta zazzabi ko tari ko kuma suna shan wahala wurin yin numfashi da su kira wadannan lambobin: 08025088304, 08032401473, 08035871662 da 08037808191;

Bugu da kari, Gwamnatin Jihar Kaduna ta umurci duk ma’aikatan gwamnati daga matakin albashi na 12 zuwa ƙasa su zauna a gidajensu na tsawon kawana 30. Kuma wannan zai fara ne daga gobe Talata 24 ga watan Maris, 2020. Amma ma’aikatan da suke aiki irin na jinya da tsaro da sauransu za su ci gaba da zuwa aiki. Muna roƙon kowa ya zauna a gida domin a taimaka a daƙile yaɗuwar wannan annoba.

Kasancewar Kasuwa wata matattara ce ta taruwan jama’a, ba a yarda wani ɗan kasuwa ya fito ba sai ‘yan kasuwan da suke sayar da kayan abinci da magunguna aka yarda su fito. Kuma jami’an tsaro da hukumar da ke kula da kasuwanni ta Jihar Kaduna za su tabbatar da an bi wannan dokar.

Gwamnatin Jihar Kaduna za ta sa ido ta tabbatar an bi wannan dokar, in ba haka ba kuma za ta sanya dokar ta baci ta hana shiga da fita a jihar baki daya.

Ya ku ‘yan uwana al’ummar Jihar Kaduna mu dauki ƙaddara domin yakar wannan annobar gaba daya mu daƙile yaduwar wannan cutar ta Korona Baros.

Na gode, Allah ya kawo mana ƙarshen wannan annoba.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.