Home / Big News / Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya Ya Kamu Da Cutar Korona

Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Nijeriya Ya Kamu Da Cutar Korona

 

Daga  Imrana Kaduna

Bayanan da ke fitowa daga tarayyar Nijeriya na cewa shugaban ma’aikatan Fadar shugaban kasa Abba Kyari, ya kamu da cutar Korona bairus.

Kamar yadda bayanan ke fitowa ana kyautata taron cewa ya kamu da cutar ne a lokacin da ya kai ziyara kasashen Jamus da Misra (Egypt) domin halartar wani taron tattaunawa a kan batun kamfanin wutar lantarki, wanda babban shugaban kamfanin Furofesa James Momoh, yana cikin taron

Shugaban ma’aikatan ya halarci tarurruka da dama bayan da ya dawo daga tafiyar a satin da ya wuce.

An bayyana cewa ABBA Kyari, ya fara yin tari ne a lokacin wani taro a ranar Lahadi a fadar shugaban kasa, abin da yasa jama’a suka rika maganganun cewa ya kamu da cutar.

Bayanan Gwajin nasa da ya fito ranar Talata da safe ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Korona bairus.

Shima shugaba Muhammadu Buhari, an Gwada shi an tabbatar yana dauke da cutar.

Zamu kawo maku karin bayani nan gaba.

About andiya

Check Also

BANDITRY: WE TOOK THE WAR TO THE NEXT LEVEL- DIKKO RADDA

By Lawal Sa’idu in Katsina In an effort to bring an end to BANDITRY and …

Leave a Reply

Your email address will not be published.