Home / Ilimi / Ganduje Ya Bayar Da Kudin Gyaran Makarantun Firamare A Kano

Ganduje Ya Bayar Da Kudin Gyaran Makarantun Firamare A Kano

Imrana Abdullahi
Kamar yadda aka Sani Gwamnati ta mayar batun ilimin Firamare da Sakandare  kyauta domin a samu ci gaban da kowa yake fatan ganin an samu.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya mikawa daukacin kananan hukumomi 44 kudin gyaran makarantun Firamare, domin yin  kai tsaye wajen gyaran makarantun.
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron da aka yi a Kano domin kaddamar da mikawa kananan hukumomi kudin da suka kama daga miliyan 20 zuwa Ashirin da doriya domin kwamitocin da aka Sanya su yi aikin gyara  kai tsaye, kuma an ba su tsawon wa’adin sati uku ne su kammala aikin.
Gwamna Ganduje ya bayyana kudin da aka ba su da suka kai miliya 88,9244,93,38 kuma kamar yadda aka ji Gwamnan na cewa za a kammal aikin ne a cikin sati uku
Sai dai Gwamna Ganduje ya bayyana nan gaba za a dawo wurin da aka yi taron mikawa kowa kudin domin kowa ya yi bayani gaban Talbiji,rediyo da yan jarida iron aikin da ya aiwatar a wurin da aka ce a gabatar da aikinn, ” in mutum ya aiwatar da aikin kamar yadda ya dace jama’a za su ji kuma za a yi masa alkalanci”.
Ganduke ya kuma yi kira ga jama’a da su guji yin aikin aika aika wanda saboda haka ne aka gayawa kowane kwamiti a kowace karamar hukuma irin aikin da zai yi don haka muna kira a guji yin aikin aika aika, saboda Gwamnati ta Sanya wadansu injiniyoyin da suka san aiki kuma za su Sanya idanu kan yadda ake yin aikin.
“Kasancewar an mayar da karatun Firamare da Sakandare kyauta a Jihar saboda Gwamnatu na ba makarantu kudin gudanar da ayyukan da za su yi domin a ciyar da Jiha tare da kasa baki daya gaba”.

About andiya

Check Also

WE MUST DEPLOY ADVANCED TECHNOLOGY TO FIGHT INSECURITY, GOVERNOR LAWAL TELLS UNITED NATIONS 

By; Imrana Abdullahi, Kaduna Governor Dauda Lawal has emphasized the pressing need to deploy advanced …

Leave a Reply

Your email address will not be published.